Uncategorized
‘Yan Hari da Makami Sun Kashe Jami’an Tsaro Biyu a Yola
Rundunar ‘yan sandan Najeriya, reshen jihar Adamawa ta tabbatar da kisan wasu ‘yan sanda biyu na Rundunar ta hannun wasu ‘yan hari da makami da ba a san ko su wanene ba a Mubi, wani gari da ke kasuwanci a arewacin babban birnin jihar Yola.
Naija News ta samu labarin cewa an kashe ‘yan sanda biyun ne a ranar Litinin da daddare ta hannun wasu ‘yan hari da bindiga da suka boye a cikin daji kusa da Titin Gyella, cikin Karamar Hukumar Mubi ta Kudu.
A cewar wata majiya, an ce an kashe jami’an ‘yan sanda biyun ne hadi da sace wasu mazauna yankin shida a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka hari ‘yan sanda da mazauna a kan hanyar Gyella.
Daga baya dai, rundunar ‘yan sanda ta ba da tabbacin cewa ba wanda aka sace yayin harin na daren Litinin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Sulaiman Nguroje, Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan sanda (DSP), ya tabbatar da kisan ‘yan sandan biyu.
Ya ce, “A daren jiya wasu jami’an ‘yan sanda da ke sintiri sun hangi wani mutum yana yawo a kan hanya, a bakin daji, suka kuwa yi la’akari da yanayin mutumin cewa bai cikin hankalinsa.”
“Jami’an sun gano da cewa mutumin ya tsere ne daga hannun ‘yan fashi. Daga nan sai jami’an suka yanke shawarar shiga cikin daji don fatattakar ‘yan fashin” Inji mutumin.
Ya kara da cewa, rundunar ‘yan sanda ta tattara darukan tsaro da yawa hadi da jami’ai da ke a Mubi da kewayenta, da iyaka yankin zuwa garuruwan da ke kusa da Jamhuriyar Kamaru don murkushe masu aikata muggan laifukar.