Connect with us

Uncategorized

Rundunar Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan Boko Haram 4

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A ranar Asabar da ta gabata, Rundunar Sojojin Najeriya sun hau ‘yan Boko Haram da hari har sun kashe mutum hudu daga cikin su.

Ganawan wutar ya faru ne tsakanin Rundunar Sojojin Najeriya da ‘yan Boko Haram a nan kauyen Malumfatori da ke yankin Abadam, a Jihar Borno inda rundunar sojoji suka lashe ‘yan ta’addan da nasara ta kashe mutane hudu da kuma ribato wasu makaman yaki daga ‘yan ta’addan.

Mun samu rahoton haka ne a tabbacin Col. Onyema Nwachukwu, mataimakin Daraktan Operation LAFIYA DOLE, da cewa ‘yan ta’addan Boko Haram sun tada wata farmaki a daren Asabar da ta gabata inda suka hade da rundunar sojojin kasar, watau Operation Lafiya Dole da ke a nan Jihar Borno.

“Rundunar sun yi musayar harsasu da ne da ‘yan ta’addan a daren Asabar har Sojojin sun kashe mutum hudu daga cikin su da ribato makaman yaki daga ‘yan ta’addan” in ji Col. Nwachukwu a bayanin sa da ya bayar a Maiduguri ga manema labarai.

“yan ta’addan sun yi gudun hijira da raunukan harsasu da suka gane da cewa rundunar na shan karfin su” in ji shi.

“Yan Ta’addan Boko Haram din sun yi kokarin kai farmaki ne da tsakar duhun daren ranar Asabar, 2 ga watan Fabrairun, 2019 amma sai suka fada hannun rundunar sojojin Operation Lafiya Dole a hake, rundunar kuwa suka hau su da wuta”

Col. Nwachukwu ya kara da cewa rundunar sojojin sun fada daji da neman sauran ‘yan ta’addan da suka yi gudun hijira.

Ko da shike an bayyana da cewa Sojoji ukku sun samu rauni sakamakon munsayar harsasu da suka yi da ‘yan ta’addan.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Rundunar sojojin Najeriya sun yi barazanar cin nasara a yaki da Boko Haram a garin Baga da ke Jihar Borno makonnai da suka wuce.