Labaran Najeriya
Matasan Jihar Benue sun fusata da ziyarar Buhari a Jihar Benue
Matasan Jihar Benue sunyi kunar Tsintsiya, Alamar rashin amincewa da Zaben Buhari
Rahoto ta bayar da cewa Matasan Jihar Benue sun fada wa Fillin Wasan Kwallon Kafa da ke a Makurdi, inda shugaba Muhammadu Buhari da Jam’iyyar APC suka gudanar da hidimar neman zabe. Matasan sun fito ne da yawan su tare da tsintsiya a hannun su wai don share bakin jini da shugaba Muhammadu Buhari ya shigo a Jihar da ita.
Muna da sani a Naija News cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya ziyarci Jihar Benue ranar Laraba 6 ga Watan Fabrairun, 2019 da ta gabata don gudanar da hidimar yakin neman sake zabe a zaben tarayya da ke gabatowa a kasar Najeriya a shekara ta 2019.
Bayan barin shugaba Muhammadu Buhari da Jam’iyyar APC a Jihar, Matasan sun fito makil da tsintsiyar su dan share filin da kuma kone tsintsiyar, watau alaman rashin amincewa da shugabancin Jam’iyyar APC.
Ko da shike muna da sani a Naija News da cewa ba shugaba Muhammadu Buhari ne kawai aka wa irin wannan ba, yawancin shugabannan kasar Najeriya sun fuskanci irin wannan zargi da kiyayya.
Karanta Wannan kuma: Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi barazanar cewa duk Kasar Waje da ta sa baki ga zaben Najeriya za ta fuskanci mutuwa.
Kalla: Yadda ‘yan Najeriya suka bayyana kiyayyar su da tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo