Uncategorized
‘Yan Boko Haram sun kashe Ali Kirim, Mai anguwar Gubla, a Jihar Adamawa
Rundunar Sojojin Najeriya da ke tsaro a yankin Madagali sun yi ganawar wuta da ‘yan ta’addan Boko Haram a yankin Madagali ta Jihar Adamawa har sojojin sun kashe daya daga cikin ‘yan ta’addan.
Ganawar wutar ya dauki tsawon awowi biyu ne tsakanin Rundunar Sojoji da ‘yan ta’addan kamin dada sojojin suka sha karfin su.
Kamar yadda mazaunan kauyen suka bayar ga manema labarai, Bayan ganawar wuta da ‘yan ta’addan suka yi da rundunar sojojin Najeriya a yankin, ‘yan ta’addan sun fada wa kauyen Gubla misalin karfe 5 na maraice a ranar Asabar da sun kashe mai anguwar Gubla, Ali Kirim.
“Karar harbin bindiga ya bi ko ta ina, kowa da ke kauyen ya yi gudun hijira zuwa kauyukan da ke kewayen har sai da safiyar ranar Lahadi da komai ya huce, sa’anan kowa ya dawo”
Mallam Yusuf Muhammad, Tsohon Ciyaman na karamar hukumar Madagali, ya tabbatas da harin, ya ce “Sun kashe Mallam Ali Kirim ne a yayin da yake kan komawa gidan sa daga garin Madagali”.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya, da cewa ‘yan ta’adda sun sace Ciyaman na Jam’iyyar APC a Jihar Adamawa
Ko da shike a lokacin da wannan harin ya faru, ba a samu bayyani daga rundunar sojojin ba da ke a Yola. Othman Abubakar, Kakakin yada yawun Jami’an tsaron ‘Yan Sanda na Jihar ya bayyana da cewa yana wata ganawa a Birnin Abuja a lokacin.
Karanta wannan kuma: Wani Manomi ya kashe ‘yar shekara 4 a Jihar Katsina