Connect with us

Uncategorized

Zan bada tallafin Mota ga duk mai bukatar zuwa gida don zabe – Reno Omokri

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wani sananen dan Najeriya da ke da suna Reno Omokri, wanda ke da wata shirin gidan talabijin na bayanin kirista ya aika a yau Litinin, 18 ga Watan Fabrairu a yanar gizon nishadarwa ta twitter da cewa, ya gane da cewa mutane da yawa basu ji dadin matakin da hukumar zaben kasa, INEC ta dauka ba, na daga ranar zaben shugaban kasa.

“Na kuma gane da cewa yawancin mutane ba su da bukatar koma yin tafiya saboda irin bacin rai da kuma kashe-kashe da suka yi wajen tafiya don su jefa kuri’ar su. Ina bada dama ga duk wanda ke son ya koma tafiya don jefa kuri’ansa, zan bada tallafin mota ko kodin mota don hakan daga aljihu na” inji Reno.

“Wannan ba shiri bace na wata Jam’iyya, ba ta APC bane ko PDP, na shirya wannan ne don Najeriya”

“Duk mai muradin tafiya ya bincika layin twitter di na @renoomokri ranar Laraba don samun cikakken bayani akan yada za a halarci wajen shigan mota”

Ya kara da cewa abin bukata kawai shine Katin zaben dan kasa. duk mai wannan, za a bayar da dama gareshi ga yin tafiya ba tare da biyar kudi ba a cikin motar da ni Reno Omokri zan samar.

Ga sanarwan a layin twitter, kamar yadda ya aika a turance;

https://twitter.com/renoomokri/status/1097485354809151488

Ganin irin wannan kyakyawar shiri na Reno Omokri, ‘yan Najeriya sun bayyana murnan su ga wannan tallafi da mutumin ya shirya.

Ga bayanin su kamar haka;

https://twitter.com/renoomokri/status/1097489436793819137