Connect with us

Uncategorized

INEC: Allah ne kawai zai iya daga zaben ranar Asabar – inji Farfesa Mahmood

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaban hukumar gudanar da zaben kasa, Farfesa Mahmood Yakubu, ya furta da cewa “Allah ne kawai zai iya dakatar da zaben shugaban kasa da ta gidan majalisa da za a yi ranar Asabar”.

Wannan shine fadin Farfesa Mahmood a wata ganawa da yayi da wata rukuni a babban birnin Tarayya, Abuja akan hidimar zaben shekarar 2019.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa hukumar gudanar da zaben kasa ta daga zaben shugaban kasa da ya kamata a yi a ranar Asabar da ta gabata zuwa ranar Asabar ta gaba, watau ranar 23 ga watan Fabrairu.

“Komai na a shirye don zaben ranar Asabar” inji Yakubu, a wata sanarwa da aka bayar daga bakin Dokta Mustapha Lecky, Kwamishanan hidimar zaben kasa.

“Hukumar ta riga ta samar da duk wata kaya da za a yi amfani da ita wajen hidimar zaben, saboda hakan ba wata abin damuwa” inji shi.

Mohammed Adamu, shugaban jami’an ‘yan sandan kasar Nejeriya ya kara bugun gaba da bada tabbacin cewa hukumar su zata samar da tsaro ta musanman ga wannan zaben.

“Zan tabbatar da cewa mun kame duk wanda ya dauki matankin sace akwatin zabe, zamu kuma dauki mataki ta musanman da irin wannan mutumin kamar yadda take a cikin dokar zaben kasa” inji Adamu.

“Zamu kuma tabbatar da cewa kowace jam’iya ta samu tsari ta kwarai ba tare da nuna bambanci ba, kuma ba zamu ci mutuncin kowa ba idan har bai aikata laifi ba” inji shi.

Karanta wannan kuma: Wani mamban Jam’iyyar APC ya janye zuwa Jam’iyyar PDP a Jihar Sokoto