Connect with us

Labaran Najeriya

Zaben 2019: Wani mamban Jam’iyyar APC ya janye zuwa Jam’iyyar PDP a Jihar Sokoto

Published

on

Daya daga cikin manyan masoyan shugaba Buhari ga zaben 2019, Sani Muhammad Gobirawa ya gabatar da janyewar sa daga Jam’iyyar APC zuwa Jam’iyyar PDP.

‘yan kwanaki ga zaben shugaban kasa, Gobirawa ya bayyana sabon zabin sa, ya yi murabus da tsohon jam’iyyar sa, ya kuma komawa Jam’iyyar PDP don goyawa dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar baya ga zaben 2019.

Mun samu gane da cewa Gobirawa ne mataimakin shugaban ‘yan Fensho ta Arewa masu yamman kasar. kuma yana dauke da matsayin Wakilin Gwiwa da Walin Dabagin Ardo ta Jihar Sokoto.

“Na janye ne daga Jam’iyyar APC zuwa PDP don na gane da cewa Jam’iyyar PDP ne kawai zasu iya kai kasar nan gaba ga shugabanci, da ni da wadanda muka janye daga APC mun samu ganewar hakan ne da kanmu ba tare da shirin wani ba” inji Gobirawa.

Ko da shike ba a bayyana sunayan sauran mutane ba, amma rahoto ta bayar da cewa ba Gobirawa ne kawai ya janye daga jam’iyyar ba, yana tare da wasu manyan mambobin Jam’iyyar APC da suka koma Jam’iyyar PDP.

“Ina kuma tabbatar da sanar ma masu shakkan hakan da cewa ina da hankali na da shekarun da ya isa in san matakin da ya dace a kowace lamari, Ina kuma iya zaban duk Jam’iyyar da ta fi a gareni” inji Gobirawa.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Shahararen dan shirin Fim na Kannywood, Adam A. Zango ya bayyana dalilin da ya sa ya janye daga Jam’iyyar APC zuwa Jam’iyyar PDP.

Karanta wannan kuma: ‘Yan Shi’a sun kara fita zanga-zanga da bukatar a sake shugaban kungiyar, El-Zakzaky