Labaran Najeriya
2019: Buhari, Atiku da wadansu na zaman sa hannu ga Takardar Yarjejeniyar Aminci da zaman Lafiya
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Alhaji Atiku Abubakar da wadansu yan takara na zaman sa hannu ga Takardar Yarjejeniyar Aminci da zaman Lafiya don Zaben 2019 dake gaba.
A samu wannan rihoto ne daga Kungiyar Yada Labarai ta Najeriya (NAN), da cewa wanna shiri ce ta Kwamitin Aminci na Duniya wanda aka yi shi a Cibiyar Harkokin Duniya ta Abuja, ranar Talata Karfe Uku 3:00 daidai. .
Wani Tsohon Majajoranci Soja mai suna Gen. Abdulsalami Abubakar ne ya jagoranci wanna zama.
An tsarafa wannan Takardar Yarjejeniyar Aminci ne domin dukan yan takaran Shugaban kasa su sa hannu dan tabbastas da zaman lafiya da kuma gudanas da zabe na kwarai ba tare da tashin hankali ba a zaben 2019 da ke gaba.
Yan takaran kuma ana bukatar su da gujewa maganganun ƙiyayya, , labarin karya, da kuma wasu halaye na tashin hankali a kasar Najeriya.
Ana bukatar halarar Shugabanan wannan kungiyoyi da kuma Ciyaman na Taron Jam’iyyun Siyasa na Nijeriya watau (CNPP) a wannan zama.
Wasu Yan Takarar Shugaban kasa kamar: Mr Donald Duke- Democratic Party (SDP); Mr Gbenga Olawepo-Hashim- Alliance for New Nigeria (ANN), Mr Omoyele Sowore-African Action Congress (AAC) and Mrs Obi Ezekwesili- Allied Congress Party of Nigeria (ACPN) na a bukace a wanna zama.
Ana bukatar wadansu kuma kamar haka domin sa hannu: Dr Obadiah Mailafia-African Democratic Congress (ADC); Prof. Kingsley Moghalu – Young Progressive Party (YPP); Pastor Chris Okotie – Fresh Democratic Party (FDP) retired Major Hamza Al-Mustapha-Peoples Party of Nigeria (PPN).
Habib Gajo-Young Democratic Party (YDP); retired Maj- Gen. John Gbor – All Progressives Grand Alliance (APGA); Ali Soyode-YES Party and Dr Davidson Akhimien-Grassroots Development Party of Nigeria (GDPN)