Uncategorized
Sabuwa: ‘Yan Hari da bindiga a Jihar Kano, a yau sun sace wani Injiniya
Mun samu sabuwar rahoto a Naija News Hausa da cewa wasu ‘yan hari da bindiga sun sace wani mutumin da ba a bayyana sunansa ba. Rahoto ta bayar da cewa ‘yan harin sun tare Injiniyan ne da direban da ke jaye da shi a misallin karfe bakwai na safiyar ranar Talata 12, ga watan Maris, 2019 a shiyar hanyar da ya ratsa ta Dangi a Jihar Kano.
An gabatar da cewa ‘yan harin hudu ne, suna kuma sanye da bakan abu da ya rufe idannun su yadda ba wanda zai iya gane su.
Da suka tari motar, sai suka kashe direban motar, suka kuma wuce da Injiniyar.
“Jami’an tsaron ‘yan sanda sun dauki gawar direban motar da ke dauke da injiniya. sun kuma tafi da gangar jikin zuwa idan ake ajiyar gawaki” inji wani mazaunin wajen da ya ke da sanin abin da ya faru a shiyar.
A halin yanzu ba cikakken bayani game da harin. amma idan hakan ya samu, zamu sanar maku a wannan layin..