Connect with us

Uncategorized

Gwamnatin Tarayya na shirin kafa Gonar Kashu a wasu Jihohin kasar Najeriya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnatin Tarayya ta gabatar a wata sanarwa da shirin kafa manyan gonar kashu a Jihohi hudu cikin jihohi 36 da muke da ita a kasar Najeriya.

Gwamnatin Tarayya ta yi hakan ke don karfafa da kuma inganta shukan kashu da kuma kirkiro hanyoyin da ‘yan Najeriya zasu samu aikin yi don karfafa tattalin arzikin kasar kuma.

Ga Jihohin da za a kadamar da gonakin, kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta gabatar;

  • Jihar Enugu
  • Jihar Benue
  • Jihar Kogi
  • Jihar Oyo

An gabatar da wannan shirin ne ga manema labarai a birnin Abuja daga bakin Ministan Hidimar Noma, Audu Ogbeh.

“Wannan shirin zai rage yadda ake watsi da kuma barnan diyan kashu a kasar, da kuma magance matsalar samar da diyan kashu a kasar Turai.” inji Ogbeh.

“Matsalar da daman muke samu ita ce samun isashen kudi don kadamar da hidimar, saboda za a kashe kudi kimanin Dala Miliyan Biyu idan har za a tsarafa gonar kashu mai juyi 10 ko ashirin a rana.”

“A halin yanzu muna shirin kafa gonar guda a Jihar Enugu, guda kuma a Jihar Benue. Zamu kuma kafa gona biyu a Jihar Oyo, biyu kuma a Jihar Kogi” inji Ogbeh.

Ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya na da shirin dakatar da zuwa kasar waje don tsarrafa diyan kashu. “Zamu fara tsarrafa diyan kashu a nan kasar Najeriya. da yardan Allah kuma, muna gwagwarmayan ganin cewa mun kafa gona biyu kamin shekara ta gaba”

“Muna nan muna tattaunawa da kasar Burazil a halin yanzu. Muna son ne mu tabbatar da cewa mun shigo a Na’urori da Injuna da zamu dinga tsarrafa diyan kashu a nan kasar mu”

“Diyan kashu na da muhinmanci wajen kara gina jiki. shekaru da daman mun yi barnan diyan kashu a kasar nan. Amma wannan karon, zamu yi shuki, mu kuma tsarrafa shi da kanmu” inji shi.

 

Karanta wannan kuma: Karya ne, ba mu daukan Ma’aikata a wannan lokacin – inji NIS