Uncategorized
‘Yan Hari sun saki Yahaya Lau bayan da suka karbi Miliyan Biyar
Mun gabatar a Naija News Hausa a wata sanarwa a baya da cewa ‘yan hari da bindiga sun sace Alhaji Yahaya Lau.
Alhaji Yahaya babban Ma’aikacin Gwamnati ne a Jihar Taraba. ‘Yan hari da bindiga sun sace shi ne ‘yan kwanaki Ukku da suka gabata a nan Jihar Taraba.
Mun samu rahoto da safiyar nan a Naija News Hausa da cewa ‘yan Hari da makamin sun saki Yahaya a missalin karfe Goma (10:30PM) na daren ranar Lahadi da ta wuce.
Daya daga cikin Iyalan Alhaji Yahaya ya bayar ga manema labarai da cewa sun biya kudi naira Miliyan biyar ga ‘yan ta’addan kamin suka saki Alhaji.
“Mun kai kudi naira Miliyan Biyar N5m a cikin wata doron daji da ke kusa da kauyan Kwando, a karamar hukumar Ardo-Kola ta Jihar Taraba missalin karfe 10 na dare kamin suka sake shi”
A kara bayyana ga manema labarai da cewa ‘yan harin, a ranar da suka sace Alhaji Yahaya, sun dauke naira Miliyan biyar a gidan sa.
Ko da shike a halin yanzu an sake shi, an kuma mayar masa da wayoyin salulan sa guda biyu da aka kwace, kamar yadda aka bayar a labarai.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Mahara da Makami sun sace Ubandoma, tsohon Ciyaman na Kungiyar Alkalan Jalingo.