Connect with us

Uncategorized

Mahara da Makami sun sace Ubandoma, tsohon Ciyaman na Kungiyar Alkalan Jalingo

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

A ranar Laraba da ta gabata, ‘yan hari da makami sun sace Mista Joel Ubandoma, Tsohon shugaban Kungiyar Alkalan Najeriya (NBA) ta yankin Jalingo.

Bincike ta bayar da cewa an sace Ubandoma ne a nan gidan sa da ke a unguwar Mayo-Dassa ta Jalingo, missalin karfe daya (1:00AM) na safiyar ranar Laraba, 27 ga watan Maris da ya gabata, kamar yadda aka bayar ga manema labarai.

Mista Boniface Iorkumbur, Sakataren Kungiyar, ya bayyana da bada tabbacin harin ga manema labarai da cewa lallai lamarin da gaske ce. “Lallai ‘yan hari sun sace Mista Joel, abin ya jijjiga mu kwarai da gaske. Mun kuma yi addu’a da cewa Allah zai kubutar da shi”

“Mun tashi ne da safiyar nan da wannan labarin bakin ciki, da cewa an sace dan uwan mu”

“Mun riga mun yi kira ga ‘yan kungiyar mu da yin addu’a da fatan cewa Allah zai kubutar da shi, ya kuma sa an sake shi ba tare da wata matsala ba. Muna kuma kira ga jami’an tsaro da su yi kokarin taimaka da bincike ko watakila su iya ribato Mista Joel” inji Boniface, a bayanin shi da manema labaran NAN.

Iyalan Mista Joel sun bayar da cewa basu karbi wata kira ba tukunnan tun lokacin da aka sace shi.

Kakakin yada labarai ga Jami’an tsaron ‘yan sandan yankin, ASP David Misal, ya bayar da cewa zasu sanar da duk wata karin bayani akan binciken su game da harin.

Karanta wannan kuma: An kashe wani garin gwada karfin maganin bindiga