Labaran Najeriya
Mahara da Bindiga sun Kashe wani Sarki a Jihar Sokoto
‘Yan Hari da Makami sun hari kauyan Balle da ke a yankin karamar hukumar Gudu ta jihar Sakkwato a ranar Talata, 7 ga watan Mayu da ya gabata, Inda rukunin ‘yan hari da bindiga suka rutsa da Sarkin garin, Aliyu Ibrahim.
Bisa bayanin wani da ya gana da lamarin, ya shaida ga manema labarai cewa, yan hari da makamin sun kone Ofishin ‘yan sanda biyu da Motocin faturo, bayan hakan ne suka ci gaba da shiga fadar Ibrahim, sarkin Balle, suka kuma harbe shi da bindiga.
Kalli Sanarwan Kisan Sarkin a kasa;
With deepest sorrow, i announce the death of the district head of Balle, Gudu LG sokoto who was slaughtered by unknown gunmen at his residence in Balle in an attack yesterday. May his soul rest in peace
The secuirity situation is worse @MBuhari @BashirAhmaad#ServiceChiefsMustGo pic.twitter.com/QubFpaQLWo
— MAGOREE (@Nasirmagori) May 8, 2019
Mai bada tabbacin ya kara da cewa “Kwaram da ‘Yan Hari da Makamin suka isa Fadar Sarkin, suka cinma kofar a kulle. Basu yi jinkiri ba, kawai sai suka hau kantangan gidan, wasu kuma na tsaye a waje. shigar su a fadar sai suka hari Sarkin da harbi har suka kashe shi, sa’anan suka gudu”
Masu zargi sun bayyan da cewa suna zargin cewa ‘Yan Hari daga kasar Nijar ne, sun so ne kawai don daukar fansa kan sarkin don bayyana su da yayi ga Jami’an tsaro akan ayukan su a yankin.
Ko da shike ba tabbacin ko Jami’an tsaro sun gane da ‘yan ta’addan ko kuma suna bincike a kai. Zamu sanar da duk wata karin bayani da ya biyo baya.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Shugaba Muhammadu Buhari yayi barazanar cewa ramuwar jikin Shugaban Jami’an Tsaron ‘Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu, alama ce na aikin da yake tukuru.