Uncategorized
Boko Haram: Leah Sharibu ta kai ga shekara 16 ga haifuwa a yau, Kwana 446 a hannun Boko Haram
A yau Talata, 14 ga Watan Mayu, daya daga cikin yaran Makarantar Chibok da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kame a baya, Leah Sharibu, ta kai ga cika shekara 16 da haifuwa.
Ka tuna da cewa Leah Sharibu ce ‘yar Kirista daya cikin kimanin ‘yan kananan ‘yan mata 110 da Boko Haram suka sace a makarantar sakandiri da ke a Chibok.
Al’ummar Najeriya Fiye da dari da ke a kasar Tarayyar Amurka (UK), sun gabatar da hidimar addu’a dukan dare don neman Izinin Allah da yantar da Leah Sharibu hade da sauran yaran da ‘yan ta’addan Boko Haram din suka ki saki.
Naija News Hausa ta samu ganewa da cewa yau ya cika ranar 449 da Leah ke a hannun Boko Haram, kuma ya ne cikawar ta ga shekaru 16 da haifuwa.
“Ku hada kai da mu a wannan hidimar addu’a da zanga-zangan neman yantarswa ga Leah da zamu yi a yau, a missalin karfe 1:00 zuwa 1:30 na ranar yau a wannan adiresi: 9 Northumberland Ave, Westminster, London WC2N 5BX.” inji sakon ‘yan Najeriya da ke a kasar UK.
Shugaban Hidimar Neman Yantarswa ga Leah (Leah Foundation), Malama Gloria Samdi-Puldu, ta kara kira ga Gwamnatin Tarayya da tunawa da alkawarin su da suka yi akan neman yanci ga Leah Sharibu.
Mun sanar a Naija News Hausa a baya da cewa Baban Leah Sharibu ya kamu da Ciwon bugun Jini