Uncategorized
Assha! So ta kai wani Fulani ga Mutuwa a Filin Sharo
Naija News Hausa ta karbi rahoton wani Matashin Fulani mai suna, Yari Inusa, da ya mutu a filin Sharo
Gidan yada Labaran nan tamu ta samu fahimta da cewa Inusa ya mutu ne a filin Sharo a yayin da yake kokarin nuna So da mazantaka ga karban bulaluwa, don nasara da wata yarinya da yake so kwarai da gaske.
Inusa ya mutu ne a Filin Hidimar Sharo da aka yi a kauyan Durmin Biri, ta karamar hukumar Kafur, a Jihar Katsina.
Naija News Hausa na da sanin cewa Hidimar Sharo, wata hidima ce da ‘yan yaren Fulani ke yi tsakanin Matasa ko duk wani namiji da ke son ya nuna mazantakar sa a taken munsayar bulala tsakanin shi da wani, don bayyana irin so da yake ga yarinyar da suke tsere a kanta, duk wanda ya ci nasara kuma sai a bashi yarinyar da Aure.
An bayyana da cewa Inusa yayi wa dan adawan sa, Saidu, jerin bulala ba tare da wata matsala ba, amma abin takaici, lokacin da ta kai ga karon Saidu da mayar da nashi bulalar, sai ya hari Inusa da bulalar a kai maimakon a bayan sa kamar yadda ake yi, bisa bayani wannan matakin Saidu ya karya dokar hidimar Sharo.
Da zarar da Saidu ya yiwa Inusa bulalar akai, kawai sai Inusa ya fada a kasa, daga suma har ga mutuwa.
Don bada tabbacin hakan, Kakakin yada yawun Jami’an Tsaron Jihar Kano, DSP Gambo Isah ya bayyana da cewa baban Inusa, da ake kira Mallam, da zarar da hakan ya faru, ya sanar da Jami’an tsaro da al’amarin, “Da hakan ne kuma muka kama Saidu” inji Isah.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa Masu Maganin Kudi sun kashe wata ‘yar yarinya mai shekaru biyar a cikin kauyen Rikoto na karamar hukumar Zuru, a Jihar Kebbi.