Uncategorized
Fada bai hana gaisuwa! Kalli Gwamnan Kano, Ganduje da Sarki Sanusi a Sallar Eid-Al-Fitr
Duk da irin jayayya da matsar da ke tsakanin Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje da Mai Martaba Muhammad Sanusi II, Naija News Hausa ta gano da hotonunan su biyu a lokacin da suka gana a Masalacin Idi, a bayan sallar Eid Al-Fitr da aka yi a ranar Talata da ta gabata a Jihar.
Wannan ya biyo ne bayan da a ranar Talata da ta wuce, Hukumar Bincike da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano ta bukaci cewa a tsige Sarki Muhammadu Sanusi II daga sarautar Jihar Kano, bisa wata laifin makirci da cin hanci da aka gane da shi a Jihar.
Ka tuna cewa mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa Gwamnan Jihar Kano ya rabar da kujerar sarauta Kano ga yanki 5, hade da ta da wadda Sanusi ke jagoranci.
A bayan wadannan matsalolin da ke tsakanin manya biyun ne aka gano Abdullahi Ganduje da Muhammadu Sanusi na gaisawa da juna a masallacin Eid, bayan da aka kamala hidimar sallah.
Kalli hotuna a kasa;