Uncategorized
Kalli yadda wani Limami ya Mutu a yayin da yake bada Lakca a wata Hidima
0:00 / 0:00
Innaa lillahi wa innaa ilayhi raajioon.
Wani Limami ya kai ga karshen rayuwa a yayin da ya fadi lokacin da yake gabatarwa a wata hidima
Naija News Hausa ta ci karo da bidiyon wani Limami da ya fadi a kasa ya kuma mutu nan take a lokacin da yake gabatarwa ga sauran ‘yan uwa Musulumai.
Abin ya faru ne a ranar Jumu’ah da ta wuce bisa rahotannai, inda Limamin mai suna Ustadh Ku Yaqub Ku Hashim ya fadi daga bagadi a lokacin da yake bada lakcha a masallacin Masjid Bukhari, Kedah, Malaysia.
Bisa bayanin da aka bayar, an bayyana ne da cewa Limamin a cikin gabatarwan da yake kamin ya mutu, ya gargadi musulumai da kusantar Allah a duk ayukan da suke, da kuma tabbatar da cewa sun mutu ne a hanya da ta dace idan rana hakan ya iso.
Limamin na kamala bayanin sa kwaram sai ya sunbuke ya fadi, anan take kuma sai ya mutu.
Abin mamaki da takaici, Limamin bai san da cewa ranar mutuwar shi ta riga ta iso ba.
Naija News ta fahimta da cewa Jumma’ar da ta wuce, watau ranar da Limamin ya mutu, itace jumma’ah ta farko a watan Shawwaal,
Kalli bidiyon a kasa;
KARANTA WANNAN; Matan Tsohon Gwamnan Jihar Taraba, Hauwa Suntai mai shekaru fiye da 50 ga haifuwa ta Auri wani matashi mai shekara 30 da haifuwa.
© 2024 Naija News, a division of Polance Media Inc.