Labaran Najeriya
Ga bayanin sabon Shugaban Gidan Majalisar Dattijai, Ahmed Lawan bayan Nasara
Sabon shugaban Sanatocin Najeriya da ya lashe zabe a ranar Talata da ta gabata, Sanata Ahmad Lawan, ya buga gaba da bada tabbaci da al’umma da cewa Majalisar Dattijai na 9 zata hada kai da Majalisar Dokoki da sauran rukunin Gwamnatin Najeriya don tabbatar da gudanar da ayuka da suka dace.
Sanata Lawan ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa, daren ranar Talata da ta wuce.
Ka tuna da cewa Lawan ya lashe tseren zaben kujerar shugaban gidan Majalisar Dattijai ne da yawar kuri’u 79, fiye da Sanata Ali Ndume, dan adawan sa mai kuri’u 28, kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa a baya.
“Mun isar da godiyar mu ga shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari da gurbin da ya bayyanar a matsayin Uba a hidimar zaben. wannan itace ban girman mu ga shugabannan kasar da Manya da ke shugabancin mun” inji Lawan.
“ziyarar mu ga shugaban ya kasance ne don bashi tabbacin cewa muna a shirye don hada kan mu a Majalisar Dattijai, da kuma gudanar da ayuka da suka dace, musanman daukan matakai masu muhinmi don cin nasara a wannan shugabanci”
Ziyarar da Lawan yayi a fadar shugaban kasa ya samu halartan mataimakin sa, Sanata Omo Agege, Sanata Ibikunle Amosun, Sanata Jubrin Barau da sauran su.
KARANTA WANNAN KUMA; Bayanin shugaba Muhammadu Buhari a zaman Liyafa da Manyan Shugabannan Kasa