Uncategorized
‘Yan Hari da Bindiga sun kashe ‘Yan Sanda 4 hade da DPO
Naija News Hausa ta karbi rahoto da harin ‘yan ta’adda a Ofishin Jami’an tsaron da ke a Agudama, karamar hukumar Yenagoa, Jihar Bayelsa, inda suka kashe jami’an tsaro hudu da DPO guda.
Bisa bayanin da aka bayar ga manema labarai, maharan sun sace makamai a Ofishin Jami’an tsaron, kamar Bindigogi da Kakin jami’an tsaron.
Ko da shike an bayyana da cewa maharan basu kashe mazauna shiyar ba, ila kawai jami’an tsaro da suka kashe.
Naija News Hausa ta fahimta da cewa abin ya faru ne a misalin karfe biyu na safiyar (2:15 am) ranar Litini, 1 ga watan Yuli, 2019.
“A washe garin ranar Litini, mun gane da cewa dan sanda guda ya samu tserewa, daya kuma da aka harbe a kafa ya rayu, ko da shike dai maharan sun tafi da makamai da kakin ‘yan sanda da suka kashe” inji jami’in tsaro da ya bada rahoto ga manema labarai.
KARANTA WANNAN KUMA; An sanar da Ranar zaben Ciyamomi da Kansiloli a Jihar Neja (Kalli kudin Fom)