Labaran Najeriya
‘Yan Fashi da Makami sun kashe a kalla Mutane 15 a Jihar Katsina
Naija News Hausa ta karbi rahoto da wata sabuwar hari da ‘yan fashi da makami suka kai a kauyuka hudu hudu a tsakanin karamar hukumar Kankara da Danmusa, a jihar Katsina, inda suka kashe kimanin mutane 15 a daren ranar Laraba da ta gabata.
Naija News ta fahimta da cewa wannan harin ya biyo ne a kasa da sa’o’i 24 da komawar Umar Musa, Magajin Daura da ‘yan hari da bindiga suka sace a baya da boye shi har tsawon watannai biyar a kangin fursunonin ‘yan fashi.
Mazauna kauyan sun bayyana da cewa ‘yan fashin sun fara kai harin ne a unguwar Nagwande a misalin karfe 4:30 na yamma, inda suka kashe mutane 4 kafin suka haura zuwa Unguwar Rabo, inda suka kashe 9, sannan daga bisani suka fada Gidan Daji inda suka dauki rayukan mutane 2 kuma duk a nan kauyukan yankin Kankara.
Manema labaran Aminiya sun gabatar a sanarwan su da cewa ‘yan hari da makamin sun fada a kauyen Maidabino dake a karamar hukumar Danmusa, a cikin misalin karfe 5:10 na yamma, suka bude wuta kan mazauna da ke saye da sayarwa a ranar kasuwar garin.
A lokacin da aka bayar da wannan rahoton, mazauna yankin sun tattara gawawwakin su kuma tashi da barazanar kama hanyar zuwa fadar Sarkin Katsina don nuna rashin amincewarsu game da kashe-kashen da mahara ke kawo wa yankin su.
A bayanin Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya tabbatar da wannan lamarin, ya ce a binciken su an kashe mutane goma sha daya ne a karamar hukumar Kankara, ya kara da cewa an harbe mutane biyu kuma a Maidabino.
Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa ‘Yan Harin da Bindiga sun saki Magajin Daura, bayan tsawon watannai biyar a fursunan ‘Yan Fashi da Makami.