Connect with us

Uncategorized

Mahara da Bindiga sun sace Dokta Bashir da ‘yan uwansa biyu a hanyar Lokoja

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta karbi rahoton cewa mahara da bindiga sun sace Dokta Bashir Zubayr da ke aiki da Makarantar Asibitin Kimiya ta Aminu Kano da aka fi sani da Aminu Kano Teaching Hospital (AKTH), hade da ‘yan uwansa biyu a kan hanyar Lokoja- Okene.

Rahotannai sun sanar da cewa ‘yan fashin sun sace Bashir ne da kannan sa biyu da ‘ya mace guda a Irepeni, babban hanya da ke Kilomita 20km da Lokoja a ranar Labara da ta gabata.

‘Yan uwa ga Doktan sun bayyana da cewa Bashir da ‘yan uwan sa sun kama hanyar zuwa Okene don hidimar Fidau, na cikar rana Arba’in (40th) ga mutuwar Tsohuwar su a yayin da maharan suka sace su.

Ka tuna mun sanar a Naija News Hausa a baya da cewa Gobarar Motar Tanki ya tafi da rayuka akallA 37 da barin mutane 101 da raunuka a Benue.