Labaran Najeriya
‘Yan Sandan Jihar Neja sun kame Matasa Uku da zargin yiwa ‘yar shekara 14 Fyaden Dole
Jami’an tsaron jihar Neja sun gabatar da kame wasu matasa Uku da suka kame a shiyar Maitumbi, babban birnin Jihar da zargin yiwa wata yarinya mai shekaru 14 ga haifuwa fyaden dole.
Bisa rahoton da Naija News Hausa ta samu a sanarwan manema labaran Northern City News, an gane da kame Abdulrahman Ahmed mai shekarun haifuwa 19 da abokannan cin mushen sa, Isyaku Umar (20) da Adamu Sani (20) a jihar ne bayan wata kirar kula da Jami’an tsaro suka karba daga mazauna shiyar.
An bayar da cewa matasan sun sace yarinyar ne suka kuma tafi da ita lungu, inda suka zalunce ta da yi mata fyaden dole.
Bincike ya nuna da cewa sun tari yarinyar ne a yayin da take kan hanya zuwa inda aka aike ta, a ranar Alhamis da ta gabata a cikin unguwar su, daga nan suka fyauce ta, dukansu kuma suka kwanta da ita.
“Anan take da maman yarinyar da aka yi wa fyade, Amina Abubakar, ta gane da al’amarin sai ta je a gurguje da sanar da hakan ga Jami’an tsaro.”
Ofisan dauka da yada labarai ga Jami’an tsaron Jihar, Mohammad Abubakar ya bada tabbaci ga manema labarai da cewa “lallai mun sami kame matasan Uku, bayan bincike kuma sun amince da laifin da ake zargin su da ita na yiwa yarinyar fyaden dole”
Ya karshe da cewa bayan sun kamala bincike za a gabatar da su a gaban Kotu don hukunta su akan dokar kasa.
KARANTA WANNAN KUMA; ‘Yan Harin da Bindiga sun saki Surukin Shugaba Muhammadu Buhari da aka sace a baya.