Connect with us

Uncategorized

‘Yan Fashi sun sace Daliban Makarantar ABU Zariya 3, hade da wasu Mutane Hudu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kimanin mutane 7, a ciki har da daliban Makarantar Jami’ar Ahmadu Bello Zariya Uku da ke karatun shekara ta Karshe, Namiji Guda da mata biyu da kuma wasu mutane hudu ne aka sace a kan babbar hanyar da ta bi ta Kaduna zuwa Abuja a ranar Litinin.

Naija News Hausa bisa rahoton da manema labarai suka samar ta fahimta da cewa an aiwatar da mugun harin sace mutanen ne a ranar Talata da ta gabata.

Ka tuna an ruwaito a labarai a baya da cewa an tashi sace tsohon gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo a ranar kuwa a bisa hanyar, ko da shike ba tabbacin ko wata kila a harin ne aka sace ‘yan makarantar, amma rahoto ya nuna da cewa hukumomin tsaro da ke biye da Gwamnan sun kokarta da kare shi daga harin.

Bisa bayanin wani mutum da ya bayar da bayani ga gidan jaridar Vanguard, ko da shike ya bukaci kada a bayyana sunansa, ya fada da cewa “Lallai yana da tabbacin yadda ‘yan fashin suka sace akalla mutane bakwan, hade da daliban jami’ar ABU guda Uku da ke karatun Shari’a”

A lokacin da aka bayar da wannan rahoton ba a riga an karbi bayani ba daga bakin Hukumar makarantar Jami’ar ABU ba ko ma a bakin jami’an tsaro.

Ko da shike a wata sanarwa da aka bayar da babu tabbaci a yau Alhamis a shafin yanar gizon Instablog9ja, an sanar da cewa an saki dalibai Uku ba tare da biyan ko sisi ba.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa ‘Yan Hari da Bindiga sun Sace Dan Majalisa, Aminu Magaji a Jihar Sakkwato.