Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a 4 ga Watan Oktoba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a 4 ga Watan Oktoba, 2019

1. Jonathan yayi Magana kan Abin da ya ke nadama game da mika mulki ga Buhari

Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya yi wasu bayanan game da yanayin da ya shafi amincewarsa da ya yi karban kadara ga zaben shugaban kasa da aka yi a shekarar 2015 a Najeriya.

A cewar Jonathan, bai taba yin nadama ba a kan matakin da ya dauka ga daukar kadara da amincewa da nasarar shugaba Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa na shekarar 2015.

2. Gwamnatin Najeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyoyi 32 da kasar South Afirka

Kasar South Afirka da gwamnatin Najeriya sun rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyi guda 32 da kuma fahimtar juna, wadanda suka shafi kasuwanci da masana’antu, kimiyya da fasaha, tsaro, noma da makamashi.

Shugaba Muhammadu Buhari a yayin da yake magana kan yarjejeniyar yace, Najeriya za ta ci gaba da kimanta alakar da ke tsakaninta da South Afirka, wacce aka sani da zama kasa ta biyu mafi girman tattalin Arziki a Afirka.

3. An Kama Mutane 21 da ke Samar da Magunguna ga ‘Yan kungiyar Boko Haram

Akalla da mutane 21 da ake zargin da samar da magunguna ga ‘yan kungiyar Boko ne hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta kama.

Naija News ta fahimci cewa, an kama wadanda ake zargi da hakan ne bayan da ma’aikatan hukumar NDLEA suka fada ga wata tasha da ke a Jalingo, babban birnin jihar Taraba, inda mutanen ke sayar wa ‘yan ta’addan magunguna.

4. Zaben Shugaban Kasa: Kotun Koli ta Ba da hukunci A shari’ar HDP kan Buhari

Kotun kolin Najeriya ta zartar da hukunci a wata kara da aka shigar game da nasarar da Shugaba Muhammadu Buhari ya samu a Kotun Shugaban Kasa kan karar Jam’iyyar Hope Democratic Party (HDP).

Naija News ta ruwaito cewa HDP da dan takarar shugaban kasar Jam’iyyar, Ambrose Owuru, sun gabatar da kara kan hukuncin da kotun daukaka kara ta shugaban kasar ta bayar, watau da yin watsi da karar da suka shigar kan kalubalantar nasarar Buhari a zaben shugaban kasa na 2019.

5. Shugaba Buhari na shirye don Gabatar Kasafin shekarar 2020 A Ranar Talata

Shugabancin Majalisar Dattawa ta bayyana lokacin da majalisar za ta karbi kasafin kudin kasar na shekarar 2020 daga hannun Shugaba Muhammadu Buhari.

Majalisar ta bayyana da cewa kasafin shekarar 2020 zai isa ga Majalisar daga hannun Shugaban kasa a ranar Talata, 8 ga Oktoba.

6. Dalilin da Yasa Ya Kamata A Watsar da Gidan Majalisar Wakilai – Okorocha

Sanata Rochas Okorocha ya ba da shawarar cewa kamata ya yi a rage yawan ‘yan majalisar wakilai da ke wakiltar kowace jiha na tarayya.

Okorocha, wanda ke wakiltar mazabar yamma ta Jihar Imo, ya bayyana hakan yayin da yake bayar da gudummawar jawabinsa ga rahoton kwamitin akan MTEF da aka yi a zauren majalisar dattijai.

Ya bayyana dalilinsa akan cewa kasar ta kasa da cinma biyan yawan kashe-kashen kudi da ake yi ga Majalisar Wakilan.

7. Ramaphosa kara Rokon Gafara ga ‘Yan Najeriyar da Sauran Kasashen Waje

Shugaban kasar South Afirka, Cyril Ramaphosa, ya sake rokon ‘yan Najeriya da sauran ‘yan kasashen waje saboda ayyukan ta’addancin da aka yi musu a lokacin hare-haren ‘yan tawaye a kasar.

A matsayinmu na gwamnatin South Afirka, mun nuna matukar nadama a kan harin da aka kaiwa wasu ‘yan kasashen waje da kuma la’antar da kowane nau’in rashin hakuri da ayyukan tashin hankali, “in ji Ramaphosa.

8. IGP Ya Ba da sabon Umarni Ga Rundunar Tsaron Kasa

Sufeto-Janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu ya yaba wa maza da jami’an rundunar ‘yan sanda ta Najeriya bisa kokarinsu na tabbatar da tsaro a kasar.

Shugaban ‘yan sandan ya kuma bayyana bukatar sake yin nazari kan tsarin tsaron kasar Najeriya domin samun kyakkyawan sakamako.

10. Kungiyar Kwadago ta Ba Gwamnatin Shugaba Buhari Ranar Karshe ga biyan Albashi mafi karanci

Kungiyar ‘yan Kwadago ta Najeriya ta ba gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari makwanni biyu don fara aiwatar da sabon mafi karancin albashi na ma’aikata ko kuma ta gwamnatin ta rungumi yajin aiki ga masana’antu a fadin kasar.

Naija News ta fahimci cewa kungiyar ta kunshi Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) da kungiyar Kasuwancin kasa (TUC).

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa a koyaushe