Connect with us

Uncategorized

Kannywood: Kalli Hotunan Fati Washa da Masoya Suka yi Allah Wadai da shi

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Sharararriyar da jaruma a shafin shirin fim a Kannywood, Fati Washa a ranar bikin samun ‘yancin kai na Najeriya da aka yi ranar Talata 1 ga watan Oktoba 2019 da ta gabata, ta fitar da wasu hotuna da masoyanta suka yi Allah wadai da ita.
Naija News Hausa ta tuna da cewa a ranar, al’ummar kasar hade da jarumai da yawa sun fito don nuna farin cikinsu da zagayowar cika ga karin shekara a samun yancin kai ga kasar Najeriya. A yayin murnan ne aka hango wasu hotuna da jaruma Fati Washa ta rabar a layin yanar gizon nishadarwa. Hotunan da a halin yanzu ya yadu a shafukan sada zumunta ya nuna inda Fati tayi ado sanye da kaya masu launin kore da fari, ma’ana masu kama da tutar Najeriya.
Sai dai, hotunan jarumar ya jawo kace nace a tsakanin al’umma inda mutane da yawa suka dinga to fa albarkacin bakinsu akan yanayin shiri da fitan jarumar a cikin hoton da ta rabar da kanta. Naija News Hausa ta kula bisa bayanin al’umma da cewa Hotunan dai kuru-kuru sun fito da surar jikinta, wannan kuma ya sa mutane da yawa daga cikin mabiyanta suka bayyana cewa jarumar ba ta sanya rigar nono ba, ma’ana ta dauki hoton ba tare da rigar nono ba, sannan kuma gashin kanta ya fito kowa yana kallo.
Kalli Hotunan a kasa;