Connect with us

Labaran Najeriya

APC/PDP: Kotu ta Sake Yin Watsi Da Karar da Atiku Da Jam’iyyar PDP Suka Gabatar

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kotun koli ta tabbatar da zaben Muhammadu Buhari a matsayin Shugaban kasar Najeriya tare da yin watsi da karar da dan takaran shugaban kasa Atiku Abubakar da Jam’iyyar PDP suka gabatar a koyu don kalubalantar nasarar Buhari a zaben watan Fabrairun 2019.

Mista Wole Olanipekun, mai bada shawara ga karar Jam’iyyar APC a kasar shugaban kasa, ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya bai tilasta dan takarar shugaban kasa ya sanya takaddun shaidarsa a matsayin shaidar cancanta ba.

Haka kazalika Olanipekun a gabatarwar ya kafa baki kuma ga batun Layin Ajiye Sakamakon Zabe da PDP ta zargi INEC da ita, da cewa kotun daukaka kara ba ta yarda da cewa akwai wata layin yanar gizo ta ajiyar sakamakon zabe ba.

Mista Lateef Fagbemi, daya daga cikin masu ba da shawara ga APC a yayin gabatarwar sa a gaban kwamitin hukuncin, ya bayyana amincewa da zancen Olanipekun, ya kuma bukaci Kotun Koli ta yi watsi da jefar da karar da PDP da dan takarar ta yi.