Labaran Najeriya
Kogi/Bayelsa: Shugaba Buhari Ya Komo Najeriya Bayan Ziyarar Kai Tsaye Zuwa Kasar Ingila
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar juma’a da yamma ya dawo kasar Najeriya bayan wata ziyarar sirri da ya kai a kasar Burtaniya.
Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ruwaito a baya da rahoton cewa ana dubin dawowar Shugaba Buhari a kasar ranar Asabar, 16 ga Nuwamba, kamar yadda shugaban ya sanar ta bakin maitaimaka masa wajen yada labarai a layin yanar gizo, Garba Shehu.
Bisa rahotanni da aka bayar, jirkin sama da ya dauko shugaban ya sauka ne a kasar a missalin karfe Goma saura kwata (9.45m) a daren ranar Jumma’a.
Da shugaban ke magana da manema labarai a yayin saukarsa a tashar jirgin Sama ta Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja, shugaban ya ce yana da niyyar yin aiki tukuru tare da yiwa ‘yan Najeriya hisabi.
Shugaban ya samu marabta daga Abba Kyari, shugaban ma’aikata ga shugaban kasa; Mohammed Bello, ministan babban birnin tarayya (FCT); Tukur Buratai, shugaban rundunar Sojoji, Mohammed Adamu, sufeto-janar na ‘yan sanda, da sauransu.