Uncategorized
Kogi: Ga Sakamakon Runfunan Zabe Da INEC ta Gabatar a Jihar Kogi a Yanzu
A yayin da ‘yan Asalin Kogi da ‘yan Najeriya ke duba da cike da tsammani, kwamishinan hukumar zaben jihar Kogi, Farfesa James Apam a halin yanzu yana karbar sakamakon ne daga kananan hukumomi shida.
Naija News ta fahimci cewa, Hukumar Zaben, INEC ta fara kirgan sakamakon zaben ne tsakankanin hukumomin tsaro, motocin sintiri da aka tura a kusa da ofishin INEC da cibiyar tattara sakamakon zabe a Lokoja.
Farfesa James Apam, kwamishinan zaben jihar Kogi ya gabatar ne d cewa a halin yanzu an samu sakamako ne daga kananan hukumomi shida don bayyanawa.
A yayin da masu sa ido, manyan shugabannin INEC suka yi zaman dirshan a cikin zauren Mahmood Yakubu inda sanarwar za ta gudana, an hana ‘yan jaridar da yawa shiga zauren. Jami’an INEC sun ce hana damar shiga aikin ‘yan jarida ya zama dole saboda rashin isheshen fili a cikin zauren.
Ka tuna da cewa hadi da sakamakon zaben ya kunshi zabe ta karo biyu ga kujerar Sanata a gundumar Kogi ta yamma.
Karanta Sakamakon Zaben Kananan Hukumomi da aka bayar a kasa;
Karamar Hukumar Ogori/Magongo
APC 3,679
PDP 2,145
SDP 244
Ijumu LG
APC 11,425
PDP 7,587
SDP 223
Karamar Hukumar Omala
APC 8,473
PDP 114,403
SDP 567
Karamar Hukumar Adavi
APC 64,657
PDP 366
SDP 279
Karamar Hukumar Igalamela/Idolu
APC 8,075
PDP 11,195
SDP 208
Karamar Hukumar Okene
APC 112,764
PDP 139
SDP 50
Karamar Hukumar Kabba/Bunu
APC 15,364
PDP 8,084
SDP 364
Karamar Hukumar Koton Karfi
APC 14,097
PDP 9,404
SDP 657