Connect with us

Uncategorized

‘Yan Hari da Bindiga Sun Kona Jagoran Matan PDP a Kogi da Wuta

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wasu da ake zargi da zaman ‘yan ta’addan siyasa sun hari malama Acheju Abuh, shugabar mata na Jam’iyyar PDP a Kwamitin kamfen na Wada / Aro  ta Jihar Kogi, suka kuwa banka mata wuta.

Naija News ta fahimci cewa an kunna mata wutan ne yayin da take gidanta a Ochadamu a karamar hukumar Ofu ta jihar Kogi sakamakon zaben gwamnoni na ranar Asabar da ta gabata.

Rahotanni sun nuna da cewa an kona Malama Abuh ne da yammacin ranar Litinin, a zargin cewa wasu ‘yan ta’addan jam’iyyar APC a Jihar ne suka aiwatar da mumunar harin.

An hari gidanta ne bisa rahoto a missalin karfe 2:00 na rana, suka kulle dukkan kofofin shiga da fitar gidan tare da zuba man fetur a gidan suka haska wa wurin wuta.

Wadanda ake zargi da zaman ‘yan ta’addan sun yi ta harbe-harbe ko ta ina don tsoratar da mazauna karkarar da kuma hana su zuwa wurin ceton matar yayin da ta ke konewa har gidan gaba daya ya kone.

Da ake magana kan lamarin sai aka tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta Kogi, William Aya, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce wannan lamarin kisa ne mutanen suka yi.

Ya kara da cewa an riga an watsar da jami’an tsaro zuwa yankin don hana sake fuskantar karin hari irin wannan.