Connect with us

Uncategorized

Kogi: Dino Melaye Ya Hari Ofishin INEC Da Faifan Bidiyo 21 Don Neman Soke Zabe

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Sanatan da aka kora kwanan nan mai wakiltar mazabar Kogi West Senatorial, Dino Melaye, a yau ya ziyarci hedikwatar Hukumar Zabe ta kasa (INEC) don neman a soke zaben ranar 16 ga Nuwamba a gundumar.

Dino a isarsa Ofishin ya samu marabta daga hannun Sakataren INEC, Rose Orianran-Anthony da kwamishina na kasa / Shugaban Kwamitin yada labarai da kwamitocin Ilimin masu jefa kuri’a, Festus Okoye.

Tsohon shugaban, Kwamitin Majalisar dattijai na Babban Birnin Tarayya, ya kasance a ofishin tare da wasu faya-fayen bidiyo guda 21 dauke da bayanai na tashin hankali da harbe-harben da ba su dace ba daga hannun wadanda ake zargin da wakilan zaben gwamnatin jihar Kogi.

Dino ya fadawa manema labarai da cewa kudurin sa na dawo da hakin sa da aka kwace “yaki ne na ba koma baya, ba sadaukarwa.”

A takardar da Melaye ya gabatar a ranar 18 ga Nuwamba, 2019, ya kasance ne da taken: “Kiran neman soke zaben mazabar Kogi ta yamma da aka gudanar a ranar 16 ga Nuwamba, 2019, a wasu yankuna”, kamar yadda lauyan sa, Tobechukwu Nweke ya shigar a karar.

Ka tuna da cewa Naija News Hausa ta ruwaito a cewa Dino Melaye ya bayyana abin da ya faru a jihar Kogi a ranar Asabar, 16 ga Watan Nuwamba din da ta gabata a matsayin yakin basasa ba zabe ba.

Ka tuna da cewa Dino ya nemi kujerar Majalisar Dattawa ta yankin Kogi ta yamma a zaben da aka yi ranar Asabar, 16 ga Watan Nuwamba a zaben Sanata da aka yi hade da ta gwamnoni a Jihar.