Connect with us

Uncategorized

APC: Kotu Ta Gurfanar Da Alhaji Danmaliki kan Zargin Batanci

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wata Kotun kolin Shari’a ta Gusau 1, a ranar Talata ta sake rike wani  jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar, Alhaji Ibrahim Danmaliki, bisa zargin batanci da tayar da tanzoma.

An gurfanar da Danmaliki ne a kan tuhumarsa da batanci.

Mai shari’a Hadi Sani, ya ba da umarnin a ci gaba da tsare Danmaliki a dakin kullen tare da dage sauraren karar zuwa ranar 12 ga Disamba 2019.

Babban Lauyan Gwamnatin Jihar, Mista Ibrahim Haruna, wanda ya gurfanar da wanda ake wa karar, ya fada wa kotun cewa wanda ake karar ya yi wata furuccin batancin suna ne ga Gwamnan jihar a cikin wata mujalla ta ranar 16 ga Nuwamba, a cikin kafofin sada zumunta.

Haruna ya yi zargin cewa wanda ake karar a cikin kafofin sadarwan kuma ya wallafa wani furcin zugin mutane da ke adawa da gwamnatin PDP a cikin jihar.

“laifukan sun saba wa Sashi na 287 da na 142 na kundin dokar Shari’ar kasar” inji Mista Haruna.

Haruna ya roki kotun da kar ta bayar da belin wanda ake karar har sai an sanya ranar da za a sake shari’ar domin hana yaduwar irin wannan lamarin.