Uncategorized
Hukumar NDLEA Ta Reshen Jihar Neja Ta Dahe Wani Mutum Da Jakunan Wiwi
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA), Reshen Jihar Neja, ta kama wani mutum daya da ake zargi da daukar nauyin kilogiram 1,072 na wasu kayan taba mai bugarwa a karamar hukumar Mokwa ta jihar.
Kwamandan NDLEA a jihar, Malama Sylvia Egwunwoke, ita ce ta sanar da hakan a cikin wata hira da ta yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya a Minna a ranar Asabar da ta gabata.
A cewar ita Egwunwoke, wanda aka kame da kuma zargin da miyakun kwayun, mutumin mai shekaru 56 da haifuwa ya fito ne daga kauyen Bangi, a karamar hukumar Mariga.
Ta bayyana da cewa an kama mutumin ne wanda ya karshe zamansa a kurkuku a ranar 8 ga Oktoba, saboda irin wannan laifin kuma, da cewa an kama shi ne bayan rahoton sirri da ya nuna cewa yana kan jigilar mugun ganyan zuwa jihar Sakkwato.
“An kame mutumin ne tun bara a kan hanyar Kontagora, tare da kilo 64kg na ganyan wiwi, kotu kuwa yanka mishi hukuncin yin shekara daya a gidan yari.”
Ta ce duk da haka hukumar ba za ta jinkirta ko ba da dakile ayyukan masu safarar muggan kwayoyi a jihar da ma kasar a baki daya ba.
Ta kuwa yi kira ga al’umma gaba daya da su bada rahoton duk wani alamun masu safarar kwayoyi ga hukumomin da abin ya shafa, don kawar da matsalar fataucin muggan kwayoyi da kuma matsalolin da ke addabar ta.