Uncategorized
‘Yan Mata Shidda Sun Mutu A Wata Hatsarin Kwale-Kwale A Jihar Kebbi
Hatsarin wani kwale kwale ya haifar da mutuwar wasu ‘yan mata shida a karamar hukumar Suru na jihar Kebbi, in ji wata sanarwa da aka bayar ta hannun kamfanin dillacin labarai na Najeriya (NAN).
Shugaban hukumar, Alhaji Umaru Maigandi ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labaran NAN a wata tattaunawa ta wayar tarho a ranar Talata.
Maigandi ya bayyana da cewa lamarin ya faru ne lokacin da kwale-kwale ya kife yayin da suke jigilar wadanda abin ya shafa a Kogin Tindifai ranar Litinin.
Bisa bayaninsa, ya ce jirgin ta bar ƙauyen Tindifai ne dauke da ‘yan mata tara zuwa yankin Fadama inda za su girbe shinkafa amma sai kwale-kwalen ta kife a kan hanya.
“Kauyen yana kusa ne da Bendu a Tundifai; suna kan tafiya zuwa girbin shinkafa a yankin Fadama lokacin da lamarin ya faru kuma ya haifar da mutuwar ‘yan mata shida.”
“Wadanda suka rasu a hadarin sun hada da ‘yan shekaru tsakanin 12 zuwa 15. Direban jirgin mai suna Umar Faruk, mai shekara 13 ya ci nasara da ceeton mutane uku da ran su” inji Shi Maigari.
Naija News Hausa ta tattara da cewa an binne marigayin ne bisa ga tsarin addinin Musulunci, da kuma jajantawa iyalan kuma hadi da tausaya wa wadanda suka tsira daga mummunan lamarin.
Maigari a yayin mayar da martani kan alamarin ya dora laifin hatsarin a kan cewa, hakan ya faru ne sabili da yawar lodi, cewa “jirgin anyi ta ne da damar daukar nauyin mutum biyar kawai, amma sai ga shi an cika ta da fasinjoji tara hadi da kaya.”
Shugaban ya ce majalisar za ta wayar da kan al’ummomin yankin duka game da hadarin yawar lodi ga kwale-kwale, musamman wadanda ke a yankin da ruwa take a jihar.