Connect with us

Labaran Najeriya

Shugaba Buhari Ya Aika da Jerin Sabbin Shugabbanin Kula da Hidimar Hajji a Majalisa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sunayen sabbin Shugabannai da membobin Hukumar Kula da Aikin Hajji ta kasa (NAHCON) ga Shugaban Majalisar Dattawa don tabbatarwa.

Hakan ya bayyana ne a cikin wata wasika da ya aika wa Majalisar Dattawa, wacce kamfanin dilancin labarai ta PRNigeria ta karba, Shugaba Buhari ya rubuta cewa:

“Bisa ga sashi na 3 (2) na Dokar Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) 2006, Ina mai farin cikin mikawa da neman tabbaci daga majalisar dattawa kan wadannan sunayen da aka zaba don matsayin Shugaba da membobin Hukumar Kula da Aikin Hajji ta kasa.”

Wanda aka nada a matsayin shugaba shine; Zikrullah (Sikiru) Olakunle Hassan daga jihar Osun (Kudu maso yamma).

Sauran kwamitocin zartarwar sun hada da Abdullahi Magaji Hardawa (Mai Bincike Aiki da Ba da lasans (Bauchi, Arewa Maso Gabas); Nura Hassan Yakasai Policy, (Ma’aikatar Kasuwanci da Kudi, Kano, Arewa Maso Yamma) da Sheikh Momoh Suleman Imonikhe (Shirye-shirye, Bincike, Bayyana kashi da Library (Edo, Kudu maso Kudu).

Membobin kai-da-kai na kamar haka; Malama Halimat Jibril, jihar Neja, Abbas Jato, jihar Borno, Garba Umar, jihar Sakkwato; Ibrahim Ogbonnah Amah, na jihar Ebonyi, Sadiq Oniyesaneyene Musa, dan jihar Delta da Uwargida Akintunde Basirat Olayinka, jihar Ogun.

Wakilan Ma’aikatar, Sashe da kuma hukumomin su ne; Shehu Dogo, Ma’aikatar sufurin jiragen sama, Nura Abba Rimi, Ministan Harkokin Waje, Rabi’il Bello Isa, Ministan Kudi, Kasafin Kudi da Tsarin Kasa, Zainab Ujudud Sheriff, Ministan Lafiya, Aminu Bako Yarima, Ma’aikatar Shige da Fice kasa da Ibrahim Ishaq Nuhu daga Babban Bankin Najeriya.

Kodashike dai, jaridar PRNigeria ta tattaro cewa za a aika da sunayen wakilan kungiyar Jamaatul Nasril Islam da Majalisar Koli ta Najeriya game da Harkokin Addinin Musulunci zuwa ga majalisar dattijai bayan an kammala tattaunawar.

Shugaba Buhari ya bukaci Majalisar Dattawa da ta hanzarta tantancewa da tabbatar da wadanda aka zaba.