Uncategorized
‘Yan Bindiga Sun Sace Mata Biyu Da Yara, Da Kuma Yiwa ‘Yan Sanda Hudu Raunuka
Wasu ‘Yan bindiga wadanda ake kyautata zaton ‘yan fashi ne, sun afkawa garin Ganye da ke karamar Hukumar Ganye na jihar Adamawa a safiyar Talata sannan kuma suka sace wasu mata masu shayarwa da yara guda uku, a gidan Alhaji Hussain, inji fadin ‘yan sanda da mazauna garin.
Wani dan uwan wanda abin ya rutsa da su wanda ba ya son a bayar da sunansa ya ce, ‘yan bindigar sun afka wa gidan Hussain ne da ke kusa da Kwalejin Gwamnatin Tarayya da misalin karfe 2:00 na safiyar Talata, inda suka yi nasara kan jami’an tsaro wajen, suka shiga gidan inda suka sace mahaifiya biyu mata da yara uku da barazanar bindiga.
“’Yan bindigar sun afka wa yankin ne da misalin karfe 2:00 na safiyar Talata, inda suka yi nasara a kan jami’an tsaro kuma suka shiga gidan inda suka sace wasu mata biyu da kuma wasu yara uku da barazanar bindiga.”
“Mazauna wurin duk sun tashi da firgita a yayin da suka ji mummunan harbe-harben bindigar da ‘yan bindigar ke yi da matsayin manyan makamai da suke amfani da shi don gudanar da ayyukansu.”
“Daga baya mun sanar da ‘yan sanda da sojoji a cikin garin kuma suka hanzarta da tarben ‘yan bindigar da harbe-harben bindiga a shiyar Buwangal.”
“A yayin musayar wuta, ‘yan sanda hudu sun ji rauni. Majiyar ta kara da cewa, ‘yan sanda da suka jikkata an garzaya da su zuwa asibiti na Ganye yayin da ‘yan garkuwan suka yi nasarar da wucewa da wadanda suka dauke.”
Lokacin da aka tuntubi kakakin ‘yan sanda a jihar, Sulaiman Nguroje ya bada tabbacin cewa abin ya faru ne a safiyar yau (Talata) lokacin da wasu mutane dauke da makamai suka mamaye gidan Alh Hussain Ahmadu da ke gefen wani Wukari Ward, cikin garin Ganye kuma suka sace matansa biyu tare da yara biyu.
“Nan da nan aka sanar da ‘yan sanda, DPO da tawagarsa sun garzaya zuwa inda lamarin ya faru amma sunci nasara a yayin da aka harbe mutanenmu hudu da suka samu munanan raunuka.” inji Afsan.
Ya kara da cewa an riga an watsar da jami’an tsaron da dama don su bi bayan ‘yan bindigar da tabbatar da kubutar da wadanda aka kama tare da kama wadanda suka sace su.