Connect with us

Labaran Najeriya

Gwamna Abdullahi Ganduje Yayi Wasu Sabbin Nadin Mukami a Jihar Kano

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya amince da nadin sabbin shugabannan ma’aikata da masu ba da shawara na musamman.

Gwamnan ya amince da nadin Hajiya Binta Lawan Ahmed a matsayin shugabar Ma’aikata wacce za ta maye gurbin Dr Kabiru Shehu, wanda ya kasance mai rikon kwarya ga mukamin, tun bayan kammala shekarun sa tare da ma’aikatan gwamnatin jihar, makonni kadan da suka gabata.

Har zuwa lokacin da aka nada ta, Hajia Ahmed ita ce Sakatariyar Ma’aikatar Kasuwanci ta dindindin a jihar.

Sanarwan nadin ya fito ne a kunshe cikin wata sanarwa dauke da sa hannun babban sakataren yada labarai ga gwamnan jihar Kano, Abba Anwar.

Sanarwar ta ce, Gwamnan ya bayyana sabon Shugaban Ma’aikata din a matsayin ma’aikaciyar gwamnati mai sadaukarwa, wanda “a koyaushe tana tabbatar da kwarewanta a matsayinta na ingatacciyar ma’aikaciyan gwamnati, wadda niyyarta ita ce ganin ci gaban ma’aikatar jihar.”

Gwamnan ya kuma yaba wa Dakta Shehu kan kyakkyawan ayyukan da ya yi a jihar, tare da lura cewa “Dr Kabiru Shehu ya taka rawar gani sosai. Ya kasance Shugaban Ma’aikata mai hali na gari da hulda da jama’a. Duk muna yi masa fatan alheri a rayuwarsa ta gaba.”

A haka gwamna Ganduje ya kuma amince da nadin wasu mashawarta na musamman.

Duba cikakken jerin sunayansu da mukaminsu a kasa:

1- Ali Baba (A Gama Lafiya)  – Mashawarci na Musamman, Harkokin Addini

2- Mustapha Hamza Buhari (Ba-Kwana) – Mai ba da shawara na musamman kan Harkokin siyasa

3. Hamza Usman Darma –  Mai ba da shawara ta musanman akan Ayyuka na Musamman

4. Tijjani Mailafiya Sanka – Mashawarci na Musamman a Majalisar Masarauta

5. Yusuf Aliyu Tumfafi –  Mai ba da shawara na musamman kan Manyan Ayuka

Gwamnan ya caje su da jajircewa wajen aiwatar da ayukansu da tabbatar da yin aiki don ci gaban jihar.

“Ina fatan za ku yi aiki tukuru domin daukar jiharmu zuwa matakin gaba. Kamar yadda kuka san cewa, kun dace dukanku da ofishin da aka sanyaku,” inji Ganduje.