Uncategorized
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata 15, ga Watan Janairu, a Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata 15 ga Watan Janairu, 2019
1. IGP Idris ya yi ritaya, an sanya AIG Adamu Mohammed a matsayin sabon IG
An umurci shugaban jami’an ‘yan sanda na da, IGP Ibrahim Idris da cewa ya je ya huta daga bautar kasar a matsayin shugaba jami’an Tsaro na ‘Yan sandan Najeriya (NPF).
Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da cewa an sanya AIG Adamu Mohammed a matsayin mai rikon kwaryan babban shugaban jami’an tsaron ‘yan sandan Najeriya.
2. CCT ta kafa kai ga shari’ar Baban Alkali CJN Walter Onnoghen
Babban Alkalin Shari’ar Najeriya, Walter Onnoghen yaki halartar Kotun wajen da ake masa karar zargin da aka yi masa.
Kamar yadda Naija News ta bayar da baya da cewa kimanin Alkalai 90, hade cikin su ne Manyan Alkalai guda 47 da wasu sauran Akalai guda 43 da Wole Olanipekun (SAN) ya jagoranta.
3. Dan takarar gwamna a Jam’iyyar APC na Jihar Kwara, AbdulRazaq ya tsere wa mutuwa a lokacin taron yakin nemar zabe a garin Ilorin
Wasu ‘yan ta’addan siyasa sun hari Mista AbdulRahman AbdulRazaq dan takarar gwamna daga Jam’iyyar APC a Jihar Kwara a ranar Lahadi da ta gabata, wanda ake zargi da cewa mambobin Jam’iyyar PDP ne.
‘Yan hari da bindigan da ake zargin su da wannan hali su halarci Ode Alfa Nda, wata anguwa cikin birnin Ilorin, babban birnin Jihar a yayin da ‘yan Jam’iyyar APC ke taron yakin zaben su, amma jami’an tsaro sun kare Abdulrazaq daga harin.
4. Hukumar EFCC sun kai karar Doyin Okupe a gaban Kotun Koli
Hukumar EFCC sun kai Dokta Doyin Okupe a kotun koli ne ranar Litinin da ta wuce a kotun da ke nan Maitama.
Naija News ta ruwaito da cewa ta bayar da rahoto a baya da cewa Hukumar sun kame Mai bada shawara da yada labaru ga Jam’iyyar PDP Dokta Doyin Okupe a nan birnin Abuja, a watan Disamba da ta gabata 2018.
5. Jam’iyyar PDP sun nada Ekweremadu da wasu don bada shawara ta musanman ga Atiku
Jam’iyyar PDP sun nada Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai Ike Ekweremadu a matsayin mai ba da shawara kan fasaha ga dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar a ranar Litini da ta gabata.
Jam’iyyar a cikin wata sanarwa da aka bayar daga hannun Sakataren yada labarai na Jam’iyyar, Kola Ologbondinya, an gabatar da dan majalisar wakilai RT. Hon. Yakubu Dogara, Mallam Sule Lamido da Sanata Ahmed Makarfi a matsayin masu bada shawarar fasaha ga Atiku Abubakar.
6. An daga karar Sanata Dino Melaye har zuwa ranar 28 ga watan Janairu, 2019
Babban Kotun Birnin Tarayya da ke a Maitama ta dakatar da karar Sanatan da ke wakiltar Yammacin Jihar Kogi, Sanata Dino Melaye don rashin kasancewan sa a gaban kotun.
Naija News ta ruwaito da cewa Dino Melaye na fuskantar shari’a don zargin kisan kai da aiwatar da halin da ba daidai ba da kuma gabatar da shaidar karya game da cewar ana son a kame shi.
7. Rundunar Sojoji sun kafa Hukumar Python Dance III a Jihar Legas da Jihar Ogun
Rundunar Sojojin Najeriya sun kafa wata sabon shirin tsaro da ake kira da Egwu Eke III, watau (Python Dance III) a ranar Litini da ta wuce, don magance matsalolin tsaro da ake da ita a Jihar Legas da Jihar Ogun kamin zaben 2019 da ke gaba.
Rundunar Sojojin sun tabbatar wa ‘yan Najeriya da tsaro mafi karfi da kyau daga nan har ma ga karshen zaben 2019.
8. Kotu ta dakatar da CCT daga ci gaba da gwajin CJN Walter Onnoghen
Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta umurci Gwamnatin Tarayya da dakatar da gwajin babban Alkalin tarayyar kasar Najeriya, Alkali Walter Onnoghen.
Naija News ta ruwaito da cewa Gwamnatin Tarayya ta hanyar Dokar kasa sun bayyana sharidu da zarge-zarge akan alkalin na bada lissafin kuɗi wadda ba daidai ba ne, har sau shida a ranar Jumma’a da ta wuce.
9. Hukumar CUPP da IPAC sun watsar da sharudan da Hukumar INEC ta gabatar
Kusan kimanin Jam’iyoyi 61 suka yi barazanar cewa zasu kai Hukumar kadamar da Zabe (INEC) a kotu sakamakon sharidu da matakan zabe da hukumar ta gabatar na zaben 2019 da ke gaba.
Jam’iyoyin a karkashin jagorancin Hukumar (CUPP) da kuma Hukumar (IPAC) sun bayana rashin amincewa da wadanan shiri da sharidun da hukumar gudanar da zabe suka gabatar a zama da kwamitin ta yi makon da ta wuce.
ku sami cikakun labarai daga Naija News Hausa