Connect with us

Uncategorized

Gwamnar Jihar Borno, Shettima ya kara buga gaba da murna da Boko Haram a Jihar

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamna na Jihar Borno, Kashim Shettima ya bayyana amincewa da fatan cewa Jihar Borno za ta komar da daukakar ta.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, 14 ga watan Janairu, 2019 a wata gonar kashu dake ke anan Jihar Maiduguri, Borno a yayin da ake kafa hukumar tsaron EGWU EKE III, watau (PYTHON DANCE) a wata Edkwata da ke nan Jihar inda gonar kashu din ta ke Maiduguri.

Kakakin Gidan Majalisar Jihar, Hon. Abdulkarim Lawan ne ya wakilci taron a inda ya yaba wa rundunar sojojin Najeriya bisa irin gwagwarmayar rundunar, da irin kokari na mazantaka da suka nuna wajen yaki da ta’addanci a Jihar.

Ya ce, “A gaskiya muna buga gaba da fahariya da rundunar sojojin Najeriya bisa ga irin kuzari da mazantaka da suka nuna wajen yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram a Jihar nan, kuma mun bada gaskiya da cewa Jihar Borno za ta dawo da daukakar ta, kuma al’ummar Jihar za su koma da zaman lafiya da murmushi” in ji shi.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Rundunar Sojojin Najeriya sunyi barazanar cin nasarar yaki da ‘yan Boko Harama a garin Baga da ke Jihar Borno.

Ya kara da cewa zai ci gaba da bada hadin gwiwa da rundunar sojojin da kuma sauran hukumomin tsaro da ke a Jihar wajen tabbatar da karin zaman tsaro, jama’ar jihar Borno na da murna da kuma bada gaskiya ga wannan shiri kuma mun tabbata da cewa shirin zai jawo mana kwanciyar hankali da zamantakewar al’uma duka a Jihar nan.

Gwamna Kashim Shettima ya bukaci rundunar sojojin da cewa su kara kuzari, karfafa da kuma mazantaka don cigaba da samun irin wannan nasarar zamar da kwanciyar hankali har ma da tabbatar da tsaro mafi kyau ganin zaben tarayya ta kusanto.

Jenar Bulama, wanda shi ma ya halarci taron da wasu manyan shugabannan jami’an tsaron da suka halarci taron, ya yaba wa Gwamnan da irin kokarin da shi ma yayi da bada hadin kai ga wannan nasaran. ya kuma ce wannan ganuwa da zama an yi ta ne don karfafa hukumar tsaron PYTHON DANCE ga cin nasara da aka samu tun da aka kafa ta a Jihar.

Jeneran ya kuma umurci dukan ‘yan ta’adda da ke Jihar da cewa, su guje wa halin ta’addanci ko kuma su fuskanci mumunar hukumci da yaki daga rundunar.

 

Karanta kuma: Hukumar Kadamar da Zabe, INEC ta gabatar da Sharidu da Matakai bakwai 7 ga zaben 2019