Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata 22, ga Watan Janairu, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata 22 ga Watan Janairu, 2019
1. Shugaba Buhari ya umarci Ngige don dakatar da Yajin Aikin Kungiyar ASUU
Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci Ministan Harkokin Jakadanci da Ayyuka, Chris Ngige, da cewa ya yi dukan kokarin sa dan kawo yajin aikin Hukumar ASUU ga ƙarshe.
Ngige ya bayyana umurnin shugaban kasan ne a wajen ganawar tattaunawa tare da Hukumar ASUU a ranar Litinin da ta gabata.
2. ‘Yan siyasa sunyi shirin sayen kuri’u ta hanyar masu sayar da abinci – inji INEC
Hukumar gudanar da zaben kasa (INEC) ta zargi ‘yan siyasa da shirin kawo masu sayar da abinci a rumfunan zabe dan sayen sayen kuri’un zabe daga masu jefa kuri’a ga babban zaben da za a gudanar.
Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zaben kasa, ya sanar da wannan ne a ranar Litinin a birnin Abuja a lokacin da marabci wakilai daga Kungiyar Kulawar Tarayya ta Turai (EU) a jagorancin Malama Maria Arena.
3. “Ya Karbi Kudi $5m daga gare Ni” – Obanikoro ya bada shaidar Fayose a Kotu
Tsohon ministan tsaron Jiha, Musiliu Obanikoro ya bada shaida akan tsohon gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose a gaban kotun tarayya a Ikoyi, Legas.
Obanikoro ya ce, “Ya Fayose ya karbi kudi kimanin Miliyan $5 daga gareni a lokacin zaben gwamnonin Jihar Ekiti a shekara ta 2014.
4. IGP Adamu ya sake tsarafa hukumar FSARS kuma ya watsar da wasu
Babban Shugaban Jami’an Tsaron ‘Yan sanda, Mohammed Adamu, a ranar Litinin ya kaddamar da ayyukan hukumar SARS wanda tsohon shugaban ‘yan sanda, Ibrahim Idris ya kafa kamin ya sauka.
Adamu, a gaggauce ya watsar da Ƙungiyar Bincike na Musamman (SIP) da kundiyar (STS).
5. An saki Sanata Melaye daga tsaro, kuma ya yi karar ‘yan sanda
An saki Sanatan Jihar Kogi, Dino Melaye daga tsaron ‘yan sanda. Bayan sake shi, sanatan ya yi kirar kara ga Jami’an ‘yan sandan Najeriya.
Ku tuna da cewa Sanata Dino Melaye yayi kusan mako biyu a kulle wajen jami’an ‘yan sanda kuma a halin yanzun an sake shi da belli a ranar jumma’a da ta wuce a babban kotun birnin Abuja akan lafiyar jikin sanatan.
6. Ya fi kyau ka huta, kuma ka bar wani ya cigaba da jagoran wannan kasar – Obasanjo ya gaya wa Buhari
Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo A wata hira da gidan labaran BBC Yoruba ya bayyana da cewa shugaba Muhammadu Buhari bai da lafiyar jiki da kuma lafiyar ruhu.
Ya kuma shawarci Buhari da cewa ya huta ya ba wani damar jagorancin kasar.
7. Kotu ta hana Buhari da AGF daga zancen cire CJN Onnoghen
Kotun Koli ta Tarayya da ke zaune a birnin Abuja, a ranar Litinin ta hana Shugaba Muhammadu Buhari da AGF Malami daga zancen cire babban Alkalin kasa, CJN Walter Onnoghen.
Alkali Inyang Ekwo ya ba da umarnin tsagaita wuta a lokacin gabatarwar karar a kotu da Hukumar Action Party ta gabatar.
8. Hukumar INEC sun yi musun cewa zasu dakatar da zabe a wasu sassa na kasar
Hukumar kadamar da zabe (INEC) ta bayyana cewa hukumar ba ta da niyar dakatar da zabe a wasu sassa don matsalolin da ke tsakanin wasu ‘yan takara a Jam’iyyun su.
Hukumar ta yi musun wanna kamar yadda muka sanar a rahoto da baya da cewa Jam’iyyar APC ba za su kadamar da zabe ba a Jihar Rivers.
9. Jami’an da suka janye daga yajin aikin za su yi nadama da hakan – in ji ASUU
Shugaban kungiyar jami’o’in Tarayya (ASUU), Farfesa Biodun Ogunyemi ya bayyana a ranar Litinin da cewa cibiyoyin da suka janye daga yajin aikin da kungiyar ASUU ta soma kuma suka ci gaba da kadamar da koyaswa a jami’un su zasu yi nadaman wannan matakin a gaba.
Ogunyemi ya sanar da wannan yayin da yake magana da mai ba da labarai, wanda ya nemi ra’ayinsa game da rashin daidaituwa a cikin ƙungiyoyi.
Shugaban ya bayyana wannan ne a yayin da yayi wata ganawa da manema labarai a inda suka nemi bayani daga gareshi.
10. An hanna Hukumar EFCC, ‘Yan sanda da DSS don kame Fani-Kayode
Kotun Koli ta birnin Abuja ta hana hukumar gwamnatin jiha da ‘yan sandan Najeriya daga kama ko kuma tsare tsohon ministan sufurin, Femi Fani-Kayode.
An bayyana da cewa Alkali John Tsoho ne ya bada wannan umarnin a ranar Litinin.
Ku sami cikakkun labaran Najeriya daga Naija News Hausa