Connect with us

Labaran Najeriya

APC: Shugaba Buhari ya nuna bacin ran sa da jama’ar da suka mutu a wajen yakin neman zabe

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana bacin ransa da wadanda suka rasa rayukan su ga yakin neman zabe da Jam’iyyar APC ta yi a Jihar Borno ranar jiya 21 ga watan Janairu, 2019.

Mun sanar a Naija News Hausa a ranar jiya da cewa Gwmnan Jihar Borno ya gabatar da ranar jiya a matsayin ranar hutu ga ma’aikata da ‘yan makaranta don marabtan ziyarar shugaba Muhammadu Buhari zuwa wajen hidimar yakin neman zabe.

Da baya muka samu rahoto da cewa Shugaba Muhammadu Buhari da mabiya bayan sa sun samu hallara a Maiduguri misalin karfe goma da rabi (10:30) na safiya. A yayin da shugaban Jam’iyyar APC na tarayya, Adam Oshiomole ya karbi saukar shugaba Buhari, Gwmanar Jihar, Kashim Shettima da sauran ‘yan Majalisar Jihar sun halarci wannan taron kuma.

Da safiyar yau mun sami tabbaci a Naija News da cewa wasu sun rasa rayukansu a wajen wannan hidimar, wasu kuma sun ji raunuka a yayin da suke kokarin dogon wuya don ganin shugaban da ‘yan Majalisu da suka halarci taron. An bayar da cewa wasu ma sun hau kan gini da tsani don su ga wannan hidimar, kokarin hakan ya jawo faduwar wasu daga cikin su harma an tattake su don yawar mutane da ke a wurin.

“Yawancin maza da mata na jam’iyyar, wadanda suka nemi ra’ayoyin majalisar dokokin, sun hau kan rufin ɗakunan, kan hakan ne wasu daga cikinsu suka fada ga wasu masu kallo”.

Shugaban kasar, Muhammadu Buhari ya bayyana tausayinsa ga wadanda suka ji rauni a wajen wannan hidimar rali na Jam’iyyar APC da aka gudanar a Ramat Square, Maiduguri, Jihar Borno.

A jiya Litini, Malam Garba Shehu mataimakin shugaban kasa wajen kafofin yada labarai ya ce Shugaban kasa ya bayyana bakin ciki game da wannan lamarin, yayi addu’a domin wadanda ke fama da raunuka a sakamakon wannan hidimar da cewa Allah ya basu cikakken lafiyar jiki.

Shugaba Buhari ya ce “Abin mamakin ne gare ni na jin cewa an rasa rayukan mutane a wajen hidimar da ranan na nan Maiduguri. Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu. “Na kuma samu tabbaci da cewa gwamnatin Jihar Borno, kungiyar Red Cross da sauran hukumomin agaji sun dauki matakai don taimaka wa mutanen da suka samu raunuka. Allah ya basu cikakken lafiyar jiki” in ji Shugaban.

Mun sami karin rahoto da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawalin zamar da isasshen tsaro a Jihar Borno da Yobe a yayin da ya ziyarci Jihar biyu ranar jiya don gudanar da yakin neman sake zaben sa a matsayin shugaban kasar karo na biyu.

Ya ce “Zani kara karfa tsaro a Jihar nan sa’anan kuma cigaba da ayukan da muka farasa a kasar a karo na biyu son kawo ci gaba a kasar Najeriya” in ji shi.

Ya kuma kara da cewa gwamnatin sa zata karafa tattalin arzikin kasar Najeriya da kuma samar da ayuka ga ‘yan Najeriya don magance rashin aikin yi a kasar.

 

Karanta wannan: Atiku na iya jagorancin Najeriya, amma ba tare da Peter Obi ba – in ji Omatsola