Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba 23, ga Watan Janairu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba 23 ga Watan Janairu, 2019

 

1. Majalisar Dokoki ta kasa ta amince da naira dubu 27,000 a matsayin sabon albashin

Kungiyar Majalisar Dokoki ta Kasa a jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, sun amince da Naira dubu ashirin da bakwai (N27,000) a matsayin sabon tsarin kankanin albashi ga ma’aikatan kasar Najeriya.

Wannan shi ne sanarwan da aka bayar a karshen zaman tattaunawa da aka gudanar a jiya Talata 22 ga Janairu, 2019 a nan birnin Abuja.

2. Ba za a kame Alkali Onnoghen ba don rashin halartan sa gaban kotun CCT – in ji Gwamnatin tarayya

Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da zargin cewa tana shirin kame babban alkalin shari’ar kasar Najeriya, Walter Onnoghen don kauracewa dokar shari’ar kotun karo na biyu.

Aliyu Umar SAN, ya ce fada a bayan zaman kotu da cewa “Gwamnati ba za ta bukaci kame Onnoghen ba don kauracewa zaman kotun kamar yadda aka bukace shi, duk da cewa doka ya bayyana da yin hakan.

3. Kai dan Makircin zabe ne – Tinubu za gayawa Obasanjo

Shugaban Jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya kwatanta tsohon shugaban kasar, Olusegun Obasanjo a matsayin mai “rikici da shirin makirci” ga zaben kasar.

Tsohon Gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu ya jefa wa Obasanjo wannan zargin na cewa tsohon shugaban na da alhakin lallace tattalin arzikin kasar nan tun daga shekarar 1999 da ta gabata.

4. Kungiyar Ma’aikatan kasa (NLC) sun ki amincewa da sabon albashin dubu N27,000

Kungiyar Ma’aikatar kasar Najeriya, watau (NLC) sun bayyana rashin amincewa su da yarjejeniya da Majalisar dokokin kasa ta yi a ranar Talata da ta gabata akan biyar N27,000 ga ma’aikata na zaman kankanin albashi.

Babban sakataren kungiyar, Dokta Peter Ozo-Eson ya bayyana ra’ayin kungiyar ne ga manema labarai a ranar Talata a birnin Abuja da cewa ba wanda ya isa ya rage ko taro daga dubu talatin (30,000) da suka amince da ita kwanakin baya.

5. Kungiyar gudanar da zaben Buhari ta yi karar Atiku da zargin biyar Miliyan 40m

‘Yan Jam’iyyar APC da ke gudanar da shirin sake zaben shugaba Buhari sun mika wata karar Miliyan 40m na zargin cewa dan takaran shugaban kasa ta Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya aiwatar da zargin karya game da shugaban da iyalin sa.

An mika karar ne a gaban Kotun Koli a birnin Abuja.

6. Babban Bankin Kasa ta bar manufofin ta ga kashi 14% kamar yada take a baya

Babban Bankin Tarayya ta kasar Najeriya, a karshen zaman Kwamitin Kuɗade (MPC) da suka yi a ranar Talata a birnin Abuja, sun bar tsarin kudin manufofin su a 14% kamar yada ta ke a da.

Wannan shine karo na goma sha biyar da za su bar tsarin kudin kamar haka

7. CJN Onnoghen ya bukaci a dakatar da gwajinsa a gaban CCT da tsawon lokatai

Babban Alkalin Shari’ar Nijeriya, CJN Walter Onnoghen ya bukaci Kotun koli (CCT) ta dakatar gwajin da ake masa akan rashin gabatar da dukiya zuwa gaba har da tsawon lokatai.

Mai bada shawararsa, Wole Olanipekun (SAN) ne ya gabatar da wannan a gaban kotu.

8. An dakatar da gwajin shugaban ‘yan Shi’a, El-Zakzaky zuwa ranar 25 ga Maris, 2019

Wata babbar kotun Jihar Kaduna ta dakatar da gwajin babban shugaban wata Kungiyar Musuluncin a Nigeria, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa ​​Zeenat.

An dakatar da gwajin shari’ar har zuwa watan Maris 25, 2019.

9. Atiku yafi Buhari kirki ko ta yaya – in ji Obasanjo

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya bayyana a wata ganuwa da manema labaran BBC da cewa dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar zai fi iya mulki da jagorancin kasar nan bisa Buhari har ma ya ninka shi sau biyu.

Obasanjo ya ce “Kowa na iya satar tattalin arzikin kasan nan kuma ya tsira idan har dan Jam’iyyar APC ne shi”

10. Ina murna mara matuka da shirin da Hukumar INEC ke yi game da zaben 2019 – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana da cewa yana da murna mara matukan gaske da irin shirye-shiryen da Hukumar gudanar da zaben kansa (INEC) ke yi don zaben 2019 da ta gabato.

Mai bada shawarwari ta musamman ga shugaban kasa, Garba Shehu ya fada da cewa shugaba Buhari ya gabatar da wannan ne a wata zaman Tarayyar Turai (EOM) da suka yi a brinin Abuja.

 

Ka sami cikakkun labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa a koyaushe.