Connect with us

Uncategorized

Sabuwa: Rajista na jarabawan JAMB zai fara 10 ga Watan Janairu 2019 – Farfesa Ishaq Oloyede

Published

on

at

Farfesa Ishaq Oloyede, Shugaban Hadadiyar Jarabawa ta Jakadanci (JAMB) ya bayyana cewa za a fitar da Fam na rajista don Jarabawan (JAMB/UTME) da aka saba yi kowace shekara a ranar 10 ga Janairu, 2019.

Jagoran, Ishaq Oloyede, ya gabatar da wannan ne a wani taro na masu kula da Cibiyoyin CBT da sauransu, a Jami’ar Legas a ranar Alhamis cewa, sayar da e-PINs don jarrabawar zai dauki tsawon makonni shida (6). Ko da yake ba a sanar da ainihin ranar da za a fara jarabawan ba tukunna.
Kwanakin baya Oloyede ya sanar da ranar 3 ga Janairu a matsayin ranar da Kungiyar za ta fara sayar da fam din, amma saboda wasu dalilai a canza ranar  zuwa 10 ga Watan Janairu, shekara ta 2018.

 

Naija News ta ruwaito Dan takarar Jam’iyyar Progressive Party (YPP) Kingsley Moghalu a yau Laraba, 19 ga watan Disamba 2018, ya bayyana cewa, Najeriya ta bukaci jagoranci daga yan tsarar zamani ta 21 don ci gaba da tsira daga matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta a halin yanzu.