Connect with us

Uncategorized

Jami’an Sojojin Najeriya sun kashe wasu ‘Yan Matan Boko Haram Uku a Jihar Borno

Published

on

Wata Sabuwar Nasarawa daga rundunar sojojin Najeriya

Sojin Najeriya sun bayyana cewa dakarunsa dake yaki da ‘yan kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar sun kashe ‘yan mata uku da suka kai harin bom a jihar Borno.

Bisa ga bayanin da aka bayar ga Naija News ta wurin Col. Onyema Nwachukwu, Mataimakin Daraktan na LAFIYA DOLE da cewa wannan ya faru ne a ranar Lahadi, 30 ga watan Disamba a yankin kauyen Kubtara a Dikwa Local Area na Jihar Borno.

“Sojojin Operation LAFIYA DOLE ranar Lahadi 30 ga watan Disamba 2018, sun yi ganawa da ‘Yan mata uku da suke shirye da tashi da bama-bamai, sojojin sun hadu da su ne a yayin da suke yawon faturo shiyan Kubtara a Yankin Dikwa na Jihar Borno. Sojojin sun kuma gano wata “Rocket Propelled Grenade” da kuma rigar da ake sanya bama-bamai a wajen ganuwar.

“Babban kwamandan soji, Lieutenant General Tukur Yusufu Buratai, ya sake yaba wa dakarun sojojin da suka yi wannan nasara, kuma ya karfafa su don su kasance masu tsayin daka, da hankali da kuma yin haquri, yayin da suke kokarin kame ‘yan ta’addan Boko Haram”. ya fadi wannan ne a ranar Litinin.

 

Naija News ta ruwaito Yan ta’addan Boko Haram sun kai Farmaki a Makalama, wata kauyen garin Gatamwarwa, dake karamar Hukumar Chibok, a Jihar Borno.