Connect with us

Uncategorized

Dankwambo ya nada sabbin Kwamishanoni shidda 6 a Jihar Gombe

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnan Jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo ya sanya sabbin kwamishanoni har guda shida ga Jihar don karfa ayukan Jihar.

Ya kuma umurce su da cewa “Ina bukatar ku da amfani da fasahar ku wajen tafiyar da aikace-aikacen ku a Jihar”

Dankwambo yayi wanna nadin ne a jiya Laraba 16, ga watan Janairu a gidan gwamnatin Jihar Gombe.

“Ina kira gareku sabbin kwamishanonin da ganin ku iya bada iya kokarin ku, ku kuma yi aiki yadda ya kamata ta ganin cewa kun samar da ci gaba a Jihar Gombe wajen aikin ku” in ji Gwamnan

Gwamnan ya kara bayyana da cewa gwamnatin sa ta saura ne da ‘yan watannai kadan da ganin cewa sun samar da ayuka da zai kawo ci gaba da kuma daukakar Jihar su.

Bayan gabatar da kwamishanonin, daya daga cikin su, Muhammad Mailumo ya bayyana godiyar su ga gwamnan Jihar da ganin wannan matsayin ya dace da su, “abin murna ne kuma abin godiya ne” in ji shi kamar yadda muka sami rahoton hakan a Naija News Hausa.

An kuma gabatar da sunayan kwamishanonin, sunayan su na kamar haka;

  1. Muhammad Mailumo
  2. Zainab Julde
  3. Ishiyaku Audu
  4. Asabe Nahaya
  5. Ezekiel Boryo
  6. Ibrahim Abubakar

Karanta kuma: Duk masu kokarin kafa kiyayya tsakani na da Buhari za su sha kunya – inji Amosun