Uncategorized
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a 18, ga Watan Janairu, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a 18 ga Watan Janairu, 2019
1. Hukumar INEC ta wallafa jerin sunayen ‘yan takara ga zaben 2019
Hukumar gudanar da zaben kasa, INEC ta wallafa sunayen ‘yan takara da za a jefa wa kuri’u ga zaben tarayya na shekarar 2019.
Jerin ya ƙunshi sunayen ‘yan takara kamar haka, Shugaban kasa, Majalisar dattijai, Majalisar wakilai da Majalisun jihohi da jam’iyyun su duka.
2. A ƙarshe dai, Atiku Abubakar ya sami shiga kasar Amurka
Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci kasar Amurka, Mu na da tabbacin hakan a Naija News Hausa.
Muna da tabbacin cewar Atiku Abubakar dan takarar kujerar shugaban kasa ta Jam’iyyar PDP ya isa kasar Amurka a ranar Alhamis 17, Janairu 2019.
3. Hukumar INEC ta ki sanya Jam’iyyar APC ga zaben ‘Yan Majalisa a Jihar Rivers
Hukumar gudanar da zaben kasa, INEC ta saki sunayen ‘yan takara na zaben majalisar kasa a Jihar Rivers.
Duk da haka, kamar yadda kotu ta bayar, Ba a sanya suna da alkalamin Jam’iyyar APC ba a cikin sunayan da suka wallafa.
4. An soke ganawan Kungiyar Gwamnonin kasa (NGF) akan rashin halarta ga tattaunawa game sabon albashin ma’aikata
An soke zaman tattaunawa da ya kamata Gwamnonin Tarrayar Kasar Najeriya (NGF) su halarta don kai ga yarjejeniya akan tsarin sabon albashi ga ma’aikatan Jihohi.
Rahoto ta bayar da cewa Gwamnonin hudu kawai suka halarci taron, a yayin da sauran gwamnonin suka aiko da mutane hudu don su wakilce su ga taron.
Naija News na da sanin cewa ya kama su yi ganawar ne a ranar Laraba da ta wuwakilci su.
5. Dalilin da ya sa Kungiyar Alkalan Kasa ba za su iya gudanar da karar Onnoghen ba – Sagay
A cewar Itse Sagay, shugaban kwamitin shawara na kasa akan cin hanci da rashawa (PACAC), Alkalan Shari’a ta kasa (NJC) ba za su iya gudanar da karar babban alkalin shari’ar kasar Najeriya, Walter Onnoghen ba, in ji shi.
Ya fadi wannan ne a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, babban dan Kwamitin Shawarar kasan Najeriya (SAN) ya ce “ko jariri ma ba zai zaci haka ba”, da cewa kungiyar alkaln kasar su gudanar da irin wannan zargin akan babban shugaban kungiyar.
6. Kotun kara ta dakatar da dan takaran Jam’iyyar APC, Tonye Cole
Kotun kara da ke a birnin Port Harcourt, babban birnin Jihar Rivers ta kaddamar da karar dan takara daga Jam’iyyar APC, Tonye Cole, da kalubalantar hukuncin shari’ar da aka yi ga Chiwendu Nworgu a Kotun Koli na Jihar Rivers wadda ya kawo sanadiyar dakatar da Jam’iyyar ga zaben yankunan duka a zabe na gaba.
7. An ci mutuncin mataimakin Kakakin Majalisar Jihar Ekiti a karo na biyu
A jiya Alhamis, an kara cin mutuncin mataimakin shugaban Majalisar Dokokin Jihar Ekiti, Mista Segun Adewumi.
A cewar rahotanni, tsigewar Mista Adewumi sakamakon wasu zargi ne da aka yi masa akan aikata wasu ayuka da ba kan doka.
8. Ba na cikin kwanciyar hankali a ofishina – in ji Remi Tinubu
Wakilin gidan Majalisar dokoki da ke wakilcin Jihar Legas, Sanata Oluremi Tinubu ya ce “Ba na cikin kwanciyar hankali a ofishi na”
Mista Remi ya gabatar da wannan ne a ranar Alhamis a yayin da yake magana a kan wani lamarin da ya faru a kwanan nan, inda aka fada wa ofisoshinsa da satar abubuwa masu mahimmanci.
9. Rundunar Sojojin sun yi nasarar da ‘yan Boko Haram a Gajiram nan Jihar Borno
Rundunar sojin Najeriya sun ci nasarar kai hari kan hare-haren da ‘yan kungiyar Boko Haram ke kaiwa a garin Gajiram da ke karamar hukumar Ngazai a nan Jihar Borno.
A wata gabatarwa da mataimakin Darakta, Harkokin Sadarwa da shugaban ‘Operation LAFIYA DOLE’, Col. Onyema Nwachukwu ya bayar, ya ce “sojojin sun kashe ‘yan ta’addan kuma sun ribato bindigogi da dama da kuma gano makamai a ranar Talata.
10. Mahara sun fada wa dan takarar Gwamnan Taraba, Sani Danladi
Jami’an tsaron ‘yan sandan Jihar Taraba sun bada tabbacin mumunar hari da wasu ‘yan ta’adda suka yi wa dan takarar Gwamnan Jihar Taraba daga Jam’iyyar APC, Sani Danladi a jiya Alhamis.
A fadin wani da yake shiyar a lokacin da mumunar abin ya faru, ya ce “Motoci shidda ne aka kone kurmus da wuta, kuma abin ya dauki tsawon awowi biyu.
samu karin bayanai daga Naija News