Connect with us

Labaran Najeriya

APC: Mutane Uku suka mutu a harin da aka yi wa dan takaran Gwamnan, Sani Danladi a Jihar Taraba

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Duk da irin kokarin da Jami’an tsaron kasa da gwamnatin tarayya ke yi akan ta’addanci da tashin hankali a kasar Najeriya, harwayau ba a daina haka mugun hari da kashe-kashe ba.

Naija News ta ruwaito a jiya da cewa Gwamnan Jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed hanna yawon yakin neman zabe a Jihar Kwara ganin irin mugun hako da hari da wasu ke kaifa ‘yan adawan su a Jihar.

Mun sami rahoto da cewa mutane ukku ne suka rasa rayukan su ga harin da aka kai wa dan takaran Gwamna a Jam’iyyar APC ta Jihar Taraba, Alhaji Sani Danladi a yayin da yake kan tafiya zuwa yankin Wukari don yakin neman zabe a ranar Laraba da ta wuce, kamar yadda muka bayar a Naija News da cewa mahara sun fada wa Sani Danladi, dan takaran Gwamnan Taraba da hari.

Musa Lawal, wani da ke a wajen da wannan mumunar abu ya faru, ya bayyana ga maneman labaran Daily Trust a kan waya da cewa, “mutane ukku ne suka rasa rayukan su sakamakon harbin bindiga da aka yi musu” a lokacin da aka hari motar da gwanan ke tafe da shi, in ji Musa.

“Wasu da dama kuwa sun sami raunuka sakamakon watsin harsasun bindiga, amma a halin yanzun ana masu kulawa a babban asibiti da ke Jalingo” inji shi.

“Wannan harin mataki ne na neman sace dan takaran” in ji Mista Aaron Artimas sakataren Jam’iyyar APC a Jihar.

Mun sami sani a Naija News da cewa Gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishaku ya bada umurnin cewa a kafa kullen shiga da fita a Jihar, na tsawon awowi goma shabiyu har sai komai ya kwanta.

Karanta kuma: Ban yi zaton zan fadi ga zaben 2019 ba – inji Shugaba Buhari

Kalla kuma: Harin da aka kai a gidan gadon babban sanatan Najeriya, Bukola Saraki