Labaran Najeriya
Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini 21, ga Watan Janairu, Shekara ta 2019
Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini 21 ga Watan Janairu, 2019
1. Obasanjo ya zargi Osinbajo game da batun Trader Moni a wata sabuwar wasika
Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo yana zargin Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo akan cewa ya jira lokaci daidai da zabe ya kusanto sa’anan ya fito da tsari samar da kudin tallafin kasuwanci ‘Trader Moni’ ga ‘yan kasuwa.
Naija News ta sami tabbaci da cewa Obasanjo ya bayyana wannan ne ga manema labarai a wata ganawa da suka yi a gidansa a ranar Lahadi da ta gabata a cikin wasikar bude da ya lika wa suna “Point for Concern and Action” wanda ya rarraba wa ‘yan jaridan a anan gidansa da ke Abeokuta, Jihar Ogun.
2. Jihar Borno ta furta ranar hutu na jama’a don ziyarar Buhari
Gwamnatin Jihar Borno ta gabatar da yau litini 21 ga watan Janairu a matsayin ranar hutu ga ma’aikata da makarantu don girmama wa ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kawo a Jihar.
Mun sami rahoto da cewa shugaba Muhammadu Buhari zai ziyarci Jihar Borno a yau litini, ganin wannan an dakatar da ma’aikata duka yau daga zuwa ofishoshin su ga aiwatar da ayukan su kamar yadda suka saba.
Kwamishinan yada labarai na Jihar, Dokta Mohammed Bulama ne ya sanar da hakan ranar Lahadi da ta gabata.
3. Hukumar ASUU sun nace akan sai sun sami tabbacin za a biya bashin albashin su kamin su dakatar da yajin aikin
Hukumar Mallaman Jami’o’i (ASUU) sun ce dole ne sai har gwamnati ta bada tabbacin biyan Naira biliyan 50 kamin su iya dakatar da yakin aikin da suka soma.
Shugaban Hukumar, Farfesa Biodun Ogunyemi ne ya sanar da wannan ga manema labaru a ranar Lahadin da ta gabata a birnin Ibadan, gaban ganawar da kungiyar zatayi tare da gwamnatin tarayya a ranar Litinin.
4. APC sun mayar da martani ga zargin da Obasanjo ke wa shugabancin Buhari
Jam’iyyar APC sun jefa wa tsohon shugaban kasar, Olusegun Obasanjo martani game da zarginsa ga gwamnatin tarayya da Shugaba Muhammadu Buhari.
Sakataren Harkokin Jakadancin na Jam’iyyar APC, Mallam Lanre Issa-Onilu a yayin da yake jawabi ga manema labaru a ranar Lahadi da yamma, ya ce fade-faden tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kasance zargin banza ne, da cewa wannan ya nuna irin mumunar shugabancin da ya yi a lokacinsa.
5. Obasanjo ya kwatanta shugaba Buhari da Abacha
Tsohon Shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya kai harin yawu ga Shugaba Muhammadu Buhari da cewa Buhari na shirin yin makirci ga zabe tarayya da ke gaba.
Obasanjo ya gabatar da wannan hujja ne ga manema labarai a wata ganawa da suka yi a gidansa a ranar Lahadi da ta gabata a cikin wasikar bude da ya lika wa suna “Point for Concern and Action” wanda ya rarraba wa ‘yan jaridan a anan gidansa da ke Abeokuta, Jihar Ogun.
6. Nnamdi Kanu ya yi barazana da shirin IPOB a zaben da ke gaba
Shugaban kungiyar ‘yan asalin Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu ya sake yin bayyana barazanar sa game da shirin shi da mambobin kungiyar na kauracewa ga babban zaben da ke gaba kasar Najeriya.
Nnamdi Kanu ya kara gabatar da wannan shirin ne a ranar Asabar da ta wuce da yamma a yayin da yake bayani a gidan rediyon Biafra. Ya ce “Za mu kauracewa babban zaben da ke gaba a yankunan Biafra” sai har idan Gwamnatin Tarayya ta biya bukatun mu.
7. John Momoh ya saki matsayin sa a zamar shugaban BON bayan gasan muhawarar ‘yan takaran shugaban kasa
Shugabar kungiyar Channels Media Group, Mista John Momoh, ya saki matsayinsa a zaman shugaban kungiyar watsa labaran Najeriya (BON).
An sanar da wannan ne a lokacin da aka gudanar da zaman muhawarar zaben shugaban kasa da Hukumar Yada Labarai Kasa suka gudanar a ranar Asabar a birnin Abuja.
8. APC: Dalilin da ya sa na kaucewa muhawarar shugaban kasar ta 2019 – Buhari
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana rashin kasancewarsa a muhawarar zaben shugaban kasa na shekara ta 2019 da aka gudanar a ranar Asabar da ta wuce da cewa wannan ya faru ne don “ayuka da suka mamaye shi”.
A ranar Asabar da ta wuce, Mun bayar a Naija News da cewa shugaba Buhari da Atiku basu halarci zaman muhawarar da aka gudanar ba.
9. Babu wata shiri don kame babban Alkali CJN Onnoghen – Inji Shugabanci
Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da fadin hadin gwiwar jam’iyyun siyasa da cewa suna da shirin kame babban alkalin shari’ar Tarayya, Alkali Walter Onnoghen.
Shugabanci sun karyace wannan fadin, sun ce karya ne da kulle-kulle, basu da wata shiri game da wannan zargin.
10. Dalilin da yasa ban halarci zaman Muhawarar takarar shugaban kasa ba – in ji Atiku
Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana dalilin da ya sa bai halarci muhawarar takaran shugaban kasar ba.
Duk da cewa Alhaji Abubakar ya na nan a wajen da aka gudanar da muhawarar, ya ce ban fito bane don dan adawa na Muhammadu Buhari bai fito bane.
Sami cikakkun labaran Najeriya a Naija News Hausa