Connect with us

Uncategorized

Mahara da Bindiga sun kame wani Dan Takaran Gidan Majalisa na APC a Jihar Edo, Michael Ohio

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Mun sami rahoto da a Naija News Hausa da cewa masu Hari da Bindiga sun kame wani dan takaran Gidan Majalisa na Jam’iyyar APC a Jihar Edo, mai suna Michael Ohio-Ezomon.

An sami tabbacin hakan ne daga bakin Ciyaman na yankin, Mista Frank Illaboya wanda ya bayyana ga manema labarai a yankin Eme-Ora a yau Alhamis 24, ga Watan Janairu, 2019 da cewa Mahara Ukku ne suka sace Michael a misalin karfe 1:00 na Asuba’i a yau Alhamis.

“Sun sace Dan takaran ne bayan da suka kashe dan sandan da ke masa tsaro, suka kuwa fiddashi ta tagar gidan”  in ji Mista Frank.

“A halin yanzun da nike ba ku wannan bayanin, layin wayarsa duk bai shiga, kuma wadanda suka sace shi basu bayyana kansu ba har yanzun”

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa wasu ‘Yan Hari da Bindiga da ba a san da su ba sun sace Onuoha, babban mai bada shawara ga Gwamna Jihar Rivers, Nyesom Wike 

Haka kuwa ‘yan kwanaki da ta wuce mun sanar da cewa Mahara sun yi wa dan takarar Gwamnan Taraba na Jam’iyyar APC mumunar hari a yayin da ya ke kan hanya zuwa wajen yakin neman zabe.

Mun sami sani da cewa an rigaya an kai gawar Dan Sanda da ke tsaron sa da aka kashe a dakin ajiye gawaki a nan yankin.

Kwamishanan Jami’an tsaron ‘Yan Sandar Yankin Edo, Mista Hakeem Odumosu ya gayawa manema labarai da cewa hukumar za ta shiga bincike ta gaugawa don ribato shi daga hannun maharan.

Karanta Kuma: Kada ku Tsorata don cutar ‘Lassa Fever’ muna daukar matakai don magance cutar, in ji Dokta Chikwe