Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata 29 ga Watan Janairu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata 29 ga Watan Janairu, 2019

 

1. Kayode Fayemi ya lashe zaben kotun koli a Jihar Ekiti

Dan takaran Gwamnan Jihar Ekiti na Jam’yyar APC, Kayode Fayemi ya lashe zaben gwamnan Jihar a kotu da aka yi ranar Litinin da ta gabata.

Farfesa Kolapo Olusola, dan takaran kujeran gwamnan Jihar na Jam’iyyar PDP ya yanka takarda kara ga Fayemi akan zaben da aka gudanar a ranar 14 ga watan Yuli da shi ya fadi ga zaben.

2. Maiyiwuwa Majalisar Dokokin Jihar Legas ta tsige Gwamna Ambode

Majalisar Dokokin Jihar Legas, ranar Litinin 29 ga watan Janairu, ta fara gudanar da zancen tsige Gwamna Akinwunmi Ambode akan rashin gudanar da tattalin arzikin jihar yadda ya dace da kuma rashin gabatar da kasafin kudin shekara ta 2019 a jihar.

Daga bisani majalisar ta bukaci Ambode ya bayyana a majalisar cikin mako daya akan kasafin kudin, wanda ya zama sanadiyar rikice-rikice tsakanin rukunin gwamnatin Jihar biyu.

3. Kungiyar ‘yan Biafra (IPOB) tace wa mambobin ta ‘ku zauna gida a yayin da shugaba Buhari zai ziyarci Jihar’.

Kungiyar ‘yan Biafra (IPOB) a jagorancin Nnamdi Kanu ta umarci mambobinta a Jihar Abia da cewa su zauna a gida a ranar Talata, a yayin da shugaba Muhammadu Buhari ke ziyarar Jihar Abia a yau.

Muna na tabbacin wannan ne a Naija News da cewa Kungiyar ta sanarwa mambobin ta da hakan a ranar Litinii da ta gabata daga bakin kakakin yada yawun kungiyar, Emma Powerful.

4. Onnoghen bai riga ya yi murabus ba – inji rukunin yada labarai

An karyata zancen cewa babban alkalin kotun Najeriya, Walter Onnoghen da aka dakatar yayi murabus da matsayin sa.

Babban mataimakin Alkali Onnoghen a kan kafofin yada labaran, Awusam Bassey ya karyata zancen fade-fade da ake da cewa alkalin ya yi murabus da matsayin sa. Yace “Wannan shirin makirci ne ga ‘yan adawansa ” in ji shi, ba gaskiya ko kadan daga wannan  zancen.

5. An dakatar da karar tsohon CJN Onnoghen ga CCT har da tsawon lokaci

Bayan da aka dakatar da Walter Onnoghen a matsayin babban alkalin Shari’ar Najeriya, Kotun Doka (CCT) a ranar Litinin ta dakatar da gwajin sa har zuwa tsawon lokatai da ba a sani ba.

A zarman kotun CCT, Alkalin da ke gudanar da karar ya dakatar da shari’ar har sai an kai ga yanke shawara kan gwajin a kotun kara.

6. Kada ka tura Najeriya cikin wata halin rikici – Atiku ya gargadi shugaba Buhari

Dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alh. Atiku Abubakar ya sake kira ga ‘yan Najeriya da su ki jefa wa shugaba Muhammadu Buhari kuri’ar su ga zaben shugaban kasa da ke gaba.

Atiku ya kara da cewa shugabancin Buhari bata bin doka kuma tana yaki da rukunin gwamnati biyu, watau Majalisai da rukunin Shari’a.

7. Hukumar DSS ta ba kudi Dala $500,000 da Lawan ya karba a hannu na – in ji Otedola

Babban maikudi da dan kasuwar kasar Najeriya, Femi Otedola ya bayyana da cewa Hukumar (DSS) sun mayar ma sa da kudi dala $500,000 da ya ba Farouk Lawan, tsohon mai gabatar da doka.

Yayi wannan bayanin ne a ranar litinin da ta gabata a gaban alkalin babban kotun tarayya, Apo. Angela Otaluka.

8. Shugaba Muhammadu Buhari zai ziyarci Jihar Imo da Abia a yau

A yayin da zaben tarayya ke gabatowa, Shugaba Muhammadu Buhari zai ziyarci jihohin kasar guda biyu a yau don yakin neman sake zabe.

Ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai zuwa Jihohin zai kasance ne a yau Talata 29 ga Watan Janaiaru, 2019, a yayin da shugaban zai sauka a filin jirgin saman Sam Mbakwe da ke birnin Owerri kamin ya kama hanya zuwa fillin wasan kwallon kafa in da za a gudanar da hidimar a Jihar Imo, daga nan sai Jihar Abia.

9. Zamu hana duk wata shirin makirci ga zaben Jihar Benue – Gwamna Ortom

Gwamnan Jihar Benue, Samuel Ortom ya bayyana da cewa duk wata shiri daga wani rukuni don yin makirci ga zaben 2019 a Jihar, lallai zasu hana wannan.

Gwamnan ya gabatar da wannan ne a yayoin da ya ke rantsar da Ciyaman da kwamishinan hukumar zabe na Jihar (BSIEC) a nan yankin Makurdi.

10. Kungiyar NBA ta umarci mambobin ta da kauracewa kotu a duk fadin kasar kan Onnogen

Kungiyar ‘Yan Shari’ar Kasa Najeriya (NBA) ta umarci mambobinta a fadin kasar da su kauracewa kotu a ranar Talata akan dakatarwa da aka wa babban Alkali, Walter Onnoghen (CJN).

Kungiyar ta yanke wannan shawara ne ranar Litinin da ta gabata a yayin da suka yi wata zaman gaggawa ta kasa (NEC) a birnin Abuja.

 

Ka sami cikakkun labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa