Connect with us

Uncategorized

‘Yan Hari da bindiga sun Kashe Insfektan ‘Yan Sanda biyu a Jihar Katsina

Published

on

at

advertisement

‘Yan Hari da bindiga sun kara wata sabuwar hari a Jihar Katsina da har sun kashe jam’ian tsaron ‘yan sandan Najeriya biyu.

Mun samu rahoto a Naija News Hausa da cewa ‘yan hari da bindiga sun kai sabuwar hari da har sun kashe Insfektan Jami’an ‘Yan Sandan Najeriya biyu a wata kauyen Magaji da ke yankin Batsari a Jihar Katsina a misalin karfe 9 na dare.

Rahoto ta bayar da cewa ‘Insfektan biyu da aka sani da suna, Bashir da kuma Ibrahim sun shiga tsaron kauyen ne sakamakon kiran tsaron da jama’ar kauyan suka bukaci yankin da shi kan irin hari da mahara ke kai masu.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Jami’an ‘Yan Sandan Najeriya a ranar 4 ga Watan Janairu, 2019 sun yi barazanar kashe wani da ake zargin sa a zaman shugaban ‘yan fashi a Jihar Katsina, watau mai suna Kane Mohammed, dan shekaru 35 da aka fi sanin sa da suna ‘Dan Mai-Keke.

An bayar da cewa maharan sun fada wa kauyen ne da harbe-harbe a yayin da suka sauko daga kan baburan su da kimanin yawan mutum hamsin (50).

“Sun kai kimanin mutum hamsin (50) da suka fado wa kauyen da harbe-harbe da har ya raunana mutane da yawa a kauyen”

“Sun kone motar ‘yan sanda guda biyu tare da Insfekta guda da suka kone da rai” inji wanni mazaunin kauyan kamar yada ya bayar.

A halin yanzun ba a sami bayani ba tukum daga bakin shugaban Jami’an tsaron Yankin.